Anguwar Di’o: Inda dalibai ba su shiga aji sai sun kai aji hudu
Makarantar firamare ta Anguwan Di’o, makarantar gwamnati ce da ke kauyen Tungan Maje a karkashin yankin Gwagwalada, amma saboda rashin isassun ajujuwa wadansu daliban makarantar ba su taba shiga cikin aji sun yi karatu ba, a tsawon shekarun da suka yi a makarantar a karkashin bishiya ake koya musu karatu.Binciken Aminiya ya gano cewa makarantar […]

Makarantar firamare ta Anguwan Di’o, makarantar gwamnati ce da ke kauyen Tungan Maje a karkashin yankin Gwagwalada, amma saboda rashin isassun ajujuwa wadansu daliban makarantar ba su taba shiga cikin aji sun yi karatu ba, a tsawon shekarun da suka yi a makarantar a karkashin bishiya ake koya musu karatu.
Binciken Aminiya ya gano cewa makarantar tana da gini daya ne mai dauke da ajujuwa biyu, kuma ginin na bilon kasa ne, wanda ba a gina shi bisa tsarin ajin koyar da karatun a zamani ba. Tun daga dalibai ‘yan aji daya har zuwa aji uku a waje ake koyar da su, har sai sun kai aji hudu sannan za su shiga cikin aji.
To sai dai kuma shugabar makarantar Anguwan Di’o, L.N. Miri, ta bayyana cewa karancin ajujuwa ne ya tilasta wa makarantar koyar da mafi yawan daliban koyon karatu a karkashin bishiya. “Babu yadda za mu yi. karancin ajujuwa ne ya sanya muke koyar da su a karkashin bishiya, sai dai ‘yan aji hudu da aji biyar ne suke shiga aji. Hatta ni kaina ba ni da ofis sai a waje nake zama.” Inji ta.
Ta bayyana cewa, makarantar na fuskartar matsaloli masu yawa, wadanda suka hada da rashin kujeru da makewayii da kuma katangar makaranta. Ta ce sun sha sanar da hukumomin da abin ya shafa amma har yanzu ba abin da ya canja.
Ta kara da cewa, hatta ginin da ajujuwa biyun da ke makarantar, al’ummar yankin ne suka gina. ‘’Domin a da dukkan daliban a waje suke karatu babu aji, daga bisani wani mai kishin yankin ya bayar da daki ake koyar da yaran.’’
Ta yi nuni da cewa rashin ajujuwan na shafar karatun daliban, domin yaran na yin kalle-kalle kuma abubuwa da yawa suna dauke musu hankula.
Hakazalika da Aminiya ta ziyarci makarantar firamare ta Kawu da ke kauyen Kawu da kuma makarantar firamare ta kaunyen Sabon Kawu da makarantar firamare da ke kauyen Padan Gwari da ke yankin Bwari ta gano cewa dukkansudalibansu suna koyon karatu ne a karkashin bishiya.
Shugaban makarantar Sabon Kawu Mista danjuma Adamu ya bayyana wa Aminiya cewa babbar matsalar da ke damunsu shi ne rashin isassun ajujuwa da rashin makewayi da karancin malamai da kuma karancin kayan aiki.
Aminiya ta tarar da wani malami mai suna Sama’ila Patrick Yakuso yana koyar da yara a karkashin bishiya, wanda ya bayyana cewa karancin ajujuwa ne suka sanya su koyar da yara a karkashin bishiya.
A kauyen Padan Gwari kuma Aminiya ta yi kicibis da wata makarantar da ake kira firamaren Padan Gwari, inda ta tarar da wani malami yana koyar da yara a karkashin bishiya, kuma wani abin mamaki allon da yake amfani da shi tagar wani aji ne da iska ta cire.
Shugaban makarantar Mista Elisha M Kwayawo ya bayyana cewa rashin allo na zamani ne ya sa suke yin amfani da tagar da iska ta cire na wani aji kuma ba su da allin rubutu da kuma abin goge rubutu.
Hakimin Padan Gwari, Ezeikel Baba shi ma ya bayyana cewa sun sha rubuta wa hukumomin da lamarin ya rataya a kansu halin da makarantar take ciki. Amma ya ce har yanzu ba a kawo musu dauki ba, sai dai dan abin da suka tara na kungiyar iyayen yara da malamai da shi suke tallafa wa makarantar.
Shi ma hakimin garin Kawu, Alhaji Salisu Ali, ya bayyana alhininsa ne dangane da halin da makarantar Kawu da Sabon Kawu suka shiga saboda rashin ajujuwa da kayan aiki da kuma karancin malamai. Inda ya ce tuni shi ma ya sanar da hukumi amma shiru kake ji, kamar an shuka dusa.
A tattaunawar da Aminiya ta yi da shugabannin kungiyoyin iyayen yara da malamai na makarantun a lokuta daban-daban, sun bayyana cewa gwamnati ba ta kawo musu dauki ba. Sai dai kuma sun bayyana cewa har yanzu suna sanya ido su ga irin daukin da za a kawo musu.
Wani malami a sashen ilimi na jami’ar Abuja, Farfesa J.B Badu, ya bayyana cewa koyar da dalibai a karkashin bishiya zai shafi kokarinsu a fannonin lissafi da turanci tare da samar da karin yaran da ba su zuwa makaranta a yankin Abuja.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Shugaban yankin Bwari da shugaban hukumar ilimi na bai -daya na yankin ya ci tura. Amma shugaban gundumar Gwagwalada, Alhaji Abubakar Giri, ya bayyana cewa biyan albashin ma’aikatan karamar hukuma da na malaman makarantun yankin shi ne alhakin da ya rataya a kansu, sai dai kuma ya ce hukumar ilimi na bai-daya ta yankin ita take da alhakin kula da kayayyakin aiki da kuma gine-ginen makarantun.
Sakataren ilimin yankin, Alhaji Usman Yahaya, ya shaida wa Aminiya cewa babban abin da hukumar yankin take yi shi ne ta kai dauki inda ake bukata.“A hakkin da ya rataya a kanmu na kai dauki, mun kai dauki makarantu da yawa, inda muka gina ajujuwa. Idan ka je ka duba za ka ga ajujuwan da muka gina muka danka su ga al’umomin yankin.” Sai dai kuma ya alakanta halin da ilimi yake ciki a yankin a kan karancin kudi.
Ya bayyana cewa samar da ajujuwa hakki ne na hukumar da ke lura da makarantu, amma a nasu bangaren sun yi duk kokarin da ya kamata don tunkarar kalubalen da ke fuskantar ilimi a yankin Gwagwalada.
Da yake karin haske dangane da lamarin, tsohon shugaban kungiyar shugabanin makarantun firamare na Abuja, Mista Okoro Jacob, ya bayyana cewa ilimin firamare na fuskantar tarin matsaloli a birnin tarayya Abuja.
Ya bayyana cewa sai gwamnati ta dauki matakan da suka dace a wajen sannan za a iya maganin matsalolin da ke damun ilimi a Abuja. Ya kara da cewa makarantu a yankunan karkara suna cikin hali ni-‘ya-su kuma ba a ba su kulawa.
Da Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun hukumar ilimi na bai-daya ta birnin tarayya Abuja, Muhammed Sani Lawal, ya ce shugabar hukumar ta yi tafiya amma idan ta dawo zai sanar da ita batun sannan kuma zai tuntubi wakilinmu. Amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai tuntubi wakilinmu ba kuma bai amsa kiran da aka yi masa ba.