Ankwa ta jawo wa fasihin yaro daukaka

Wani fasihin yaro mai suna Ahmed Mohammed da aka daura wa ankwa saboda kera agogon bango ya samu daukaka a Amurka, inda Shugaba Barack Obama ya aike masa da sako ta Tweeter tare da alkawarin ganawa da shi a watan gobe.Hukumar makarantarsa ce ta zarge shi da yunkurin kera bam kuma ta mika shi ga […]

Ankwa ta jawo wa fasihin yaro daukaka
Ankwa ta jawo wa fasihin yaro daukaka

Wani fasihin yaro mai suna Ahmed Mohammed da aka daura wa ankwa saboda kera agogon bango ya samu daukaka a Amurka, inda Shugaba Barack Obama ya aike masa da sako ta Tweeter tare da alkawarin ganawa da shi a watan gobe.
Hukumar makarantarsa ce ta zarge shi da yunkurin kera bam kuma ta mika shi ga ’yan sandan Jihar Tedas, bayan da ya kera agogon bango a gida, ya kai makarantar don nuna wa ’yan uwansa dalibai da kuma malamarsu ta kere-kere irin bajinta da ya yi.
A ranar Litinin ne Ahmed Mohammed mai shekara 14, ya tafi makarantarsu da ke garin Irbing a Jihar Tedas cike da farin cikin kera agogon, amma sai ya hadu da fushin hukumar makarantar wadda maimakon ta yaba masa, sai ta kira ’yan sanda suka kama shi.
“Na kera wannan agogon ne don in burge malamata, amma da na nuna mata, sai ta dauka wata barazana ce ga rayuwarta,” inji Ahmed lokacin da yake ganawa da manema labarai. “Wannan hakika abin takaici ne ganin yadda ta yi wa al’amarin mummunar fahimta,” inji shi. Ahmed ya tattauna da manema labarai da suka taru a kofar gidansu, sanye da wata ’yar riga da aka rubuta sunan cibiyar Nazarin Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) a lokacin da aka kama shi.
“Sun kama ni, inda suka yi mini bayanin cewa, na aikata laifin kera bam din bogi don tsoratar da mutane,” kamar yadda ya shaida wa kafar labarai ta WFAA bayan an sako shi. Mai magana da yawun ’yan sanda, James McLellsn ya ce: “Mun yi kokarin yi masa tambayoyi, amma amsar da kawai yake ba mu ita ce agogo ne.”
A shekaranjiya Laraba ne’yan sandan suka yanke hukunci cewa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu ko a tuhume shi da wani laifi ba.
Wani babban jami’in ’yan sandan, Larry Boyd, ya ce, sun fahimci cewa yaron bai yi nufin tsoratar da kowa ba, kuma ya bayyana kere-keren yaron a matsayin “gwajin gida,” da ba ya da wata cutarwa. Burin Ahmed shi ne ya samu shiga Cibiyar Nazarin kere-kere (MTI) da ke Massachusset a Amurka.
Yaron ya ce bai damu cewa, ’yan sanda ba su nemi afuwarsa ba, amma ya koka kan yadda ’yan sandan suka tuhume shi ba a gaban lauya ba.
Lauyarsa Linda Moreno, ta bayyana wa manema labarai cewa, ba za su amsa wata tambaya ba, game da dokokin shari’a.
Shugaban Amurka Barack da ’yar takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar Democrat, Hillary Clinton da Sakataren Ilimi na Amurka, Ame Duncan da dubban mutane sun nuna goyon bayansu ga Ahmed.
“Agogon bango mai kyau, Ahmed,” kamar yadda Obama ya rubuta shafinsa na Tweeter. “Ko za ka kawo shi fadar White House? Wannan aiki naka zai bayar da kwarin gwiwa ga suaran yara irinka, ta yadda za su rika sha’awar kimiyya. Wannan al’amari ne da ya haifar wa Amurka daukaka.”
Shugaban ya bukaci ya gana da yaron, tare da sauran masana kimiyya a Fadar White House, cikin wata mai kamawa, inda za a yi bikin shekara na daren nazarin taurari, a cewar Sakatare Watsa Labarai na Fadar White House, Josh earnest.