Annoba ta hallaka dalibai hudu a Unity School da ke Gumi

dalibai hudu ne suka rasu sakamakon bullar wata annoba da ba a gano musabbabinta ba, a makarantar hada-ka da ke garin Gumi a karamar Hukumar Gumi da ke Jihar Zamfara.Cutar dai wadda wasu suke ganin ta samo asali ne daga abinci ko ruwan sha, tana haifar da mummunan zazzabi da gudawa ga daliban, kuma bayan […]

Annoba ta hallaka dalibai hudu a Unity School da ke Gumi
Annoba ta hallaka dalibai hudu a Unity School da ke Gumi

dalibai hudu ne suka rasu sakamakon bullar wata annoba da ba a gano musabbabinta ba, a makarantar hada-ka da ke garin Gumi a karamar Hukumar Gumi da ke Jihar Zamfara.
Cutar dai wadda wasu suke ganin ta samo asali ne daga abinci ko ruwan sha, tana haifar da mummunan zazzabi da gudawa ga daliban, kuma bayan rasuwar daliban hudu akwai 19 da suke fama da cutar inda biyar daga cikinsu nasu ciwon ya fi tsanani, kuma suna karbar magani a Asibitin Tarayya da ke Gusau.
Wadanda suke jinya a Gusau hukumar asibitin ta kebe su a wani wurine na musamman da ba a barin jama’a su gansu, kuma wakilinmu da ya ziyarci asibitin cikin ayarin manema labarai da aka hana su ganin marasa lafiyar kai tsaye, ya bi ta wata hanya, inda ya ga daliban biyar an sanya wa kowanensu kunzugu kuma suna fama da kumburin fuska da kafafu.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa saura mutum 12 da suka rage an killace su a wani wuri a garin Gumi kuma ana kula da su domin gudun yaduwar cutar, kuma tuni an rufe makarantar.
Shugaban Hukumar Ciyar da dalibai Malam Atiku Sani Maradun, ya ki yin bayani lokacin da manema labarai suka tuntube shi, sai dai su tafi asibiti inda aka kwantar da marasa lafiyar.
daya daga cikin manyan jami’an asibiti da  a ce a sakaye sunansa, ya bayyana wa wakilinmu cewa ana gudanar da bincike don gano musabbabin wannan annoba, kuma a cewarsa gwamnati ta samar da isassun magunguna don kula da wadanda abin ya shafa, sai dai ya nemi a rika kula sosai domin a cewarsa wannan cutar ba ta rasa nasaba da abinci ko ruwan sha.
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Zamfara Alhaji Umar Bukkuyum ya bayyana wa manema labarai cewa cutar ba annoba ce da ta faru saboda sakaci ba, an banagren abinci ko ruwa kamar yadda wasu suke cewa sai dai annoba ce daga Allah.
Ya ce mutum biyu ne suka rasu kuma dalibai ne suka kamu da cutar kuma suna Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Gusau ana kula da su, yadda ya kamata. Ya ce akwai kwararrun likitoci da suke gudanar da bincike a kan annobar, kuma da zarar sun gano musabbabinta to za su dauki mataki cikin gaggawa.