Annobar da ta fi COVID-19 na nan tafe – WHO

Hakan na zuwa ne ‘yan makonni bayan hukumar ta ayyana kawo karshen COVID-19

Annobar da ta fi COVID-19 na nan tafe – WHO

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus (Hoto: France24)

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta gargadi mutanen duniya da su shirya wa wata annoba da ta fi cutar COVID-19 muni nan ba da jimawa ba.

Shugaban hukumar, Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ne ya bayyana hakan ranar Talata, yayin taron lafiya na duniya karo na 76 da yake gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland.

A cewarsa, “Akwai barazanar wata sabuwar nau’in cuta mai saurin yaduwa kuma mai saurin kisa, kuma har yanzu akwai barazanar cewa wannan cutar na iya bulla.

“Ba wai annobar cututtuka kawai muke fuskanta ba a duniyarmu yanzu haka. Shi kansa tsarin lafiya na duniya cikin tsananin bukata, kuma ya zama wajibi a tashi tsaye domin magance kalubalansa,” in ji shi.

Gargadin na zuwa ne ’yan makonni bayan Shugaban na WHO da kansa ya bayyana kawo karshen cutar ta COVID-19 a matsayin wata annobar ta duniya.

Sai dai ya ce babban taron na bana a kan lafiya wata babbar dama ce ga shugabanni a kowanne mataki su fito da nagartattun hanyoyi wajen magance su.

Bai dai bayyana sunan cutar ba, amma ya bukaci kowa da kowa da ya yi kyakkyawan shiri wajen yin maganinta a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos