Cutar murar tsuntsaye ta ɓulla a Kano
Gwamnatin Tarayya sanar da ɓullar cutar murar tsuntsaye a Ƙaramar Hukumar Gwale Jihar Kano.
Gwamnatin Tarayya sanar da ɓullar cutar murar tsuntsaye a Ƙaramar Hukumar Gwale Jihar Kano.
Sanarwar da Babban Jami’in Lafiyar Dabbobi ta Najeriya, ya fitar ta ce cutar murar tsuntsayen tana yaɗuwa ne a tsakanin kaji da agwagi da zabbi da talotalo.
Sanarwar da ke ɗauke da sa hannun Dakta Taiwo Olasoju ta ci gaba da cewa akwai babbar barazanar yaɗuwar cutar murar tsuntsayen daga Kano zuwa wasu sassan Najeriya.
Don haka ya bukaci gwamnatocin jihohi da ofishin lafiyar dabbobin jihohinsu da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace da kuma bin su sau da ƙafa domin daƙile yaɗuwar cutar.
- EFCC ta kama jami’an Gwamnatin Katsina kan sace tallafin N1.3b
- ’Yan ɗaurin aure 19 daga Kano sun rasu a hatsarin mota a Filato
- NAJERIYA A YAU: “Wannan Ce Ɗaya Daga Cikin Ummul Haba’isin Lalacewar Najeriya”
Ya kuma buƙaci a wayar da kan jama’a da nasu kiwo da kasuwancin tsuntsaye kan hatsarin cutar da matakan kariya, sannan hukumomi su riƙa sanya ido sosai tare da kai rahoto idan aka ga wata alama ga hukumomin da suka dace.
Dakta Olasoju ya ce ya kamata a ɗauki matakan ne a Kano da ma faɗin Najeriya.
Shugaban Ƙungiyar Masu Kiwon Kaji na Jihar Kano, Dakta Usman Gwarzo ya tabbatar da ɓullar cutar da cewa, “a cikin watan Disambar 2024 wani ɗalibin sakandare daga unguwar Galadanci a Ƙaramar Hukumar Gwale ya je Kasuwar Janguza da ke Ƙaramar Hukumar Tofa inda ya sayi agwaga ya kai gida ya sanya a cikin kajinsa sa yake kiwo a kejin katako.
“Sai agwagwar ta mutu, daga baya kajin suka bi ta, don haka ya kai gwarwwakin asibitin dabbobi na Gwale inda aka yi gwajin sakamakon ya fito ranar 1 ga watan Janairu, 2025. Amma bayan shi ba a samu makamancin hakan ba a wani gidan kaji kuma a Jihar Kano,” in ji Dakta Gwarzo.
Ya ce ƙungiyar tana aiki da Gwmanatin Jihar Kano domin wayar da kan jama’a da masu kiwon kaji domin kai rahoton duk inda aka ga alamar cutar ko mutuwar kaji da ba a aminta da shi ba.