Anthony Joshua ya doke Francis Ngannou a damben ƙwararru a Saudiyya

A yanzu Joshua na fatan zama zakaran duniya a gasar dambe a karo na uku.

Anthony Joshua ya doke Francis Ngannou a damben ƙwararru a Saudiyya

Fittaccen ɗan damben Nijeriya da Birtaniya, Anthony Joshua, ya yi nasara a fafatawar da ya yi ranar Juma’a da Francis Ngannou a Saudiyya.

An dai yi fafatawar ce a birnin Riyadh a wani gagarumin wasan dambe tsakanin shahararren ɗan damben da kuma Ngannou ɗan ƙasar Kamaru.

Karawar da aka yi mai taken “Knockout Chaos” a Turancin Ingilishi ta ƙayatar da ’yan kallo da aka fafata a filin wasa na Kingdom Arena da ke birnin na Riyadh.

A yanzu Joshua na fatan zama zakaran duniya a gasar dambe a karo na uku, bayan ya samu nasarar doke Ngannou mai shekara 34 a turmin farko da na biyu na karawar.

Bayan wannan nasara a kan Ngannou, Joshua ya fara jiyo ƙamshin shiga gasar damben boxing ta duniya wato International Boxing Federation (IBF), inda zai fafata da ɗan ƙasar Crotia da aka ayyana a matsayin ɗan damben duniya Filip Hrgovic.

Duk da shan kashi da ya yi Ngannou ba kanwar lasa ba ne a wasan dambe, musamman idan aka kalli irin rawar da ya taka a fafatawarsa da Tyson Fury a watan Oktoban 2023.

Yayin da Joshua ya kai Ngannou ƙasa a fafatawar ta Knockout Chaos

Dama Joshua ya rasa kambinsa na WBA da WBO da kuma IBF, bayan da sau biyu yana shan kaye a hannun Oleksandr Usyk a 2021 da 2022.

Akwai lada mai tsoka a wannan wasan, inda Joshua zai samun kusan dala miliyan 50 a dalilin wannan nasara, shi kuma Ngannou zai samu dala miliyan 20 da a ce shi ne ya yi nasara.

Karawar Joshua da Ngannou dai wani zakaran gwajin dafi ne kan abin da zai faru tsakanin sa da Fury, kuma nasarar da Joshuan ya samu wata manuniya ce ta fatan ƙara tabbata gwarzo a wasan damben Birtaniya.

A watan Disamba Joshua ya doke Otta Wallin, ɗan ƙasar Sweden ɗin da ya zamo wa Tyson Fury ƙarfen ƙafa a tsawon shekara huɗu.

Za a ɗauki lokaci mai tsawo duniyar damben zamani ba ta manta da gwarazan da suka fafata a fagen daga kamar Tyson Fury da Anthony Joshua ba, musamman ta la’akari da yadda sunayen su suka zamo tamkar wani suna ne na wasan damben.

Ɗan bindiga ya harbe alƙalai 2 a harabar Kotun Ƙolin Iran

’Yan Yahoo sun harbe jami’in EFCC har lahira a bakin aikinsa

Farashin kayan abinci ya faɗi warwas a Neja

Gaza: Yadda za a yi musayar fursunonin Palasdinawa da Isra’ila