Anya Alu bai ji kunya ba?
Kwanaki kadan bayan dakatar da Gwamnan Jihar Sakkwato Alu Wamakko daga jam’iyyar PDP da uwar jam’iyar da ke Abuja ta yi, ce-ce kuce da an yi an ce ya biyo baya tsakanin magoya bayan Wamakkon da kuma bangaren ‘yan Adawa a jihar. Ce-ce kucen ya samo asali ne sanadiyar kalaman da gwamnan ya gabatar ga […]
Kwanaki kadan bayan dakatar da Gwamnan Jihar Sakkwato Alu Wamakko daga jam’iyyar PDP da uwar jam’iyar da ke Abuja ta yi, ce-ce kuce da an yi an ce ya biyo baya tsakanin magoya bayan Wamakkon da kuma bangaren ‘yan Adawa a jihar. Ce-ce kucen ya samo asali ne sanadiyar kalaman da gwamnan ya gabatar ga magoya bayansa a matsayin martani zuwa ga uwar jam’iyyar.
Kalaman da suka fi daukar hankali daga cikin kalaman gwamnan, sun hada da kakkausar sukar da ya riqa yi ga shugaban jam’iyyar na qasa Alhaji Bamanga Tukur, inda har ta kai maigirman gwamnan ya yi wata addu’a gwanar ban sha’wa, ‘’Allah Ya isar wa Arewa ga Bamanga’’ in ji Alu. Wannan addu’ar kuma ta bayar da mamaki matuqa.
A daidai lokacin da magoya bayan Alu suke cewa Ameen, su kuma ‘yan adawa sai suka fashe da dariya: ‘’Shin Allah Ya isarwa Arewa ga su ALU DA SU BAMANGA? Ko kuma Allah Ya isarwa Arewa ga daukacin gwamnoni da ‘yan majalisar PDP?’’ Domin a cewarsu, Alun yana daga cikin gwamnonin da suka samarwa Ebele da kashi 25 cikin 100 na quri’un da aka jefa a zaben shekarar 2011! Don haka babu dalilin ya ware kansa don ya ga reshe na neman juyewa da mujiya.
Sannan kuma idan aka kwatanta da barnan da su Bamanga suka dade suna tafkawa Arewa da qasa baki daya da wannan barnar ta dakatar da Alu da suka yi rana tsaka daga jam’iyyarsu ta PDP, shin wace barna ce ta kai a fito a yi addu’ar tsinuwa da Allah Ya isa akanta? To amma kuma ba a ji bakin gwamnan ba sai da jifar ta kawo kansa. Wannan dalilin ne ya sa ‘yan adawa a jahar suka fashe da dariya maimaikon su ce Ameen.
Har ila yau, gwamnan ya saki baki yana magana a fusace, inda ya bayyana cewa, Sakkwatawa Alu suke so ba PDP ba, kuma idan aka ce an kore Alu daga PDP wa za a bai wa ita ke nan! Don haka su suna nan PDP daram ba gudu ba ja da baya sai an ci an cinye. Wadannan kalaman ma sun haifar da nasu tasirin a bakin al’umma, inda wasu ke cewa: ‘’Assha, gwamna girma ya fadi’’ wasu kuma sai kirari suke ta yi ga Alun, ‘’ Alu manyan duniya, an kore shi ya qi koruwa’’.
To abin lura anan shi ne, duk wani dan ranke-ranken mutum da PDP ke masa barazanar kora, yakan sha jinin jikinsa ne ya dawo roqon gafara. Amma shi kan gwarzon gwamnan ya dage kai da fata ba zai bawa kowa haquri ba. Qare da qarau ma duk wani mai jin kamar ya isa ya kore wani daga PDP ko kuma ya sa a kore shi, to gwamnan ya yi mai wankin babban bargo.
Amma fa, me yasa gwamnan zai yi magana kuma kai tsaye ya warware ta? Ya tabbatar da cewa Sakkwato shi ake so ba PDP ba, me ya sa ba zai barta baya ba, ya kama gabansa, don ya nuna musu zai iya yi ko ba su ba? Ni dai shi ne kawai abin da bai yi min dadi ba, da har ya sa nake tambaya, Shin anya Alu bai ji kunya ba?
Za a iya samun Muhammadu Nasiru Abbas
08024576898