Anya kasashen Larabawa na yin tunani kuwa?
A cikin watanni shida da suka gabata, an halaka biyu daga cikin hamshakan, kuma muhimman ’yan siyasa a kasar Tunisiya. Wannan ne ma ya sanya ’yan neman canji daga al’ummar kasar suka fantsama kan tituna, suna neman cewa a kan dole gwamnati ta sauka daga karagar mulki. Bukatarsu dai ita ce. Lallai ne a dawo […]
A cikin watanni shida da suka gabata, an halaka biyu daga cikin hamshakan, kuma muhimman ’yan siyasa a kasar Tunisiya. Wannan ne ma ya sanya ’yan neman canji daga al’ummar kasar suka fantsama kan tituna, suna neman cewa a kan dole gwamnati ta sauka daga karagar mulki. Bukatarsu dai ita ce. Lallai ne a dawo da Shugaba Ben Ali kan mulki, domin su samu damar ‘sheke ayar ’yanci’ kamar yadda su ke ikirari.
A yayin da al’ummar Tunisiya suka kasance cikin tarzoma da gwagwarmaya, takwarorinsu na kasar Masar, abin da suka maida hankali a kai ke nan. A kullum sai cika filaye suke, suna zanga-zangar neman canjin shugabanci. A kullum Dandalin Tahrir da sauran fagage irinsa sai cika suke da Larabawan da ke wannan tada jijiyar wuya. A sanadiyyar haka, rayuka na ta salwanta, tattalin arzikin kasar na ta balbalcewa; harkokin mulki da sauransu sun tsaya cik! Babu zaman lafiya, babu sukuni ga ’yan kasa, babu shi ga masu mulki.
Jerin zanga-zangar da ake fafatawa ta sanya babu aikin yi, babu sana’a. Hatta baki ’yan yawon shakatawa da ke shigowa kasar, suna samar wa Masar kudin shiga mai yawa, sun ja da baya, saboda tsoro, sakamakon tashin hankalin da ya mamaye kasar. Batun hauhawar talauci kuwa, ba a cewa komai. A yadda al’amura suke, ina ganin akwai ma ’yan kasar da ke da tunanin a dawo da Hosni Mubarak kan mulki, domin kuwa a lokacinsa, al’amura ba su tabarbare haka ba.
Wannan al’ada ta tarzoma da zanga-zanga dai ta zama yayi ga kasashen Larabawa. Al’amarin dai ya samo asali ne tun daga kan Iraki, a shekarun baya. Kada ka raba daya biyu, shaidanin da ya baibaye kan masu zanga-zangar nan, ya samu daurin gindi ne daga kasashen Turai da Amurka. Sun lura da yadda Iraki ta kasance kasa mai daula, mai dadin zama da kwanciyar hankali, don haka suka kitsa mata kutungwila, har ta kai ga matsayin lalacewa. Haka kuma, su ne suka tarairayi ’yan tawaye, suka kitsa farfaganda, suka wadata su da makamai, suka tashi tsaye har suka ga bayan gwamnatin Gaddafi. Sun kuwa ga bayan Gaddafi, Libya kuwa ta daidaice. Kaico!
Tun daga lokacin da aka ga bayan Gaddafi kuwa, babu sauran zaman lafiya a Libiya. Al’umma sun rarrabu bisa ra’ayoyi daban-daban, tashe-tashen hankali da rashin tabbas sun mamaye kasar. Idan ba a bi a sannu ba, kila za a dau dogon lokaci al’amura ba su daidaita ba. A yadda al’amura suke a yamutse, al’umma na firgice, ina ganin akwai wasu daga cikin al’ummar Libya da ke addu’ar da ma a ce Gaddafi ya dawo, domin kuwa a lokacinsa, babu irin wadannan matsalolin.
Gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah! Ga dukkan alamu, al’ummar Siriya ba su dauki darasi daga Irak da Libiya ba. Idan ba haka ba ai da ba su shashance sun dauku da neman canjin gwamnati ba. Lallai da bai kamata a ce sun zabi sun shiga tarzoma da zanga-zanga ba, domin kuwa sun ga yadda wadannan kasashe da na ambata a baya suka kasance. Ga shi yanzu sun tsoma kansu da kasarsu cikin mawuyacin hali, inda suka dauki makamai, suka fantsama suna yakar gwamnatin Bashar al-Assad. A sakamakon haka, sai ga shi kasar da aka sani da bunkasa da yalwa, ta zama kuntatatta da rashin tabbas.
A yau a Siriya da sauran kasashen Larabawa da suka wawantu, suka biye wa farfagandar ’yan barandan Turawan Yamma, suka amince da zuga, suka amince da amsar ‘taimakon makamai’ sun jefa kasashensu da al’ummarsu cikin kaka-ni-kayi. A yau, Larabawa na zubar da jinin Larabawa ’yan uwansu, suna lalata dukiyoyinsu da kasashensu da hannuwansu.
Ga wani abin takaicin kuma daga kasashen Larabawa: Dubi dai yadda gwamnatocin Saudiyya da na katar ke taimakon ’yan tawaye da makamai da kudi, wai domin su yi nasarar yakar Shugaba Bashir al-Assad! Kuma an rasa wani mai hankali da tunani da zai sanar da gwamnatocin na Saudiyya da na katar cewa, mutanen da ake halakawa a kullum, ’yan uwansu ne Larabawa, kasashensu ne, makwabtansu ne, ba baki ne ba, ba ’yan ci-rani ne ba.
Su a ganinsu, Bashir al-Assad, duk da cewa Balarabe ne, amma akidarsa ta bambanta da tasu, don haka dole ne a kore shi daga kujerar mulki. Saudiyya da katar sun manta da cewa shi ma fa Balarabe ne, addininsu daya kuma Allah daya yake bauta wa.
Haka kuma, abin ban haushi shi ne, har yanzu babu wani mai tunani da zai yi tambaya, ko mece ce ribar wannan mataki na zanga-zanga da neman sauyin gwamnatoci a kasashen Larababawa? A ganinsu, suna son kawo karshen mulkin-mulaka’u, domin maye shi da dimokradiyya. To, wane tabbaci ke gare su, cewa wadanda za su zo, za su fi na baya adalci da iya mulki? Ga shi kuma wajen neman canjin, sai kashe mutane ake yi, ana salwantar da dinbin dukiya, ko kwalliya za ta iya biyan kudin wannan sabulun?
Idan har gaskiya ne cewa idan an canja gwamnati, za a samu ci gaba, to me ya sanya ba a samu ba a kasashen Iraki da Libya da Masar, duk kuwa da cewa an tunbuke gwamnatocin da ake ganin na zalunci ne? Anya bai kamata Larabawa su sake tunani ba? Bai kamata su gane cewa al’ummarsu ake salwantarwa ba? Bai kamata su gane cewa da dukiyoyinsu ake sayen makamai ana halaka su ba? Anya kuwa kasashen Larabawa suna tunani? To ya dace su farka, su fara tunani mai kyau, domin ceto al’ummarsu daga makircin Turawan Yamma da Amurka!