APC ba za ta iya rike kasar nan ba – Salisu Kuit

Tsohon Kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Jigawa kuma Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Salisu Mamuda Kuit, ya musanta zargin da ake yi masa cewa Naira biliyan takwas ta salwanta a lokacin da yake rike da ma’aikatar a zamanin mulkin gwamnatin Alhaji Sule Lamido.Alhaji Salisu kuit babu wata shaida da ta nuna ya saci kudin […]

APC ba za ta iya rike kasar nan ba – Salisu Kuit
APC ba za ta iya rike kasar nan ba – Salisu Kuit

Tsohon Kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Jigawa kuma Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Salisu Mamuda Kuit, ya musanta zargin da ake yi masa cewa Naira biliyan takwas ta salwanta a lokacin da yake rike da ma’aikatar a zamanin mulkin gwamnatin Alhaji Sule Lamido.
Alhaji Salisu kuit babu wata shaida da ta nuna ya saci kudin da ake tuhumarsu idan kuma akwai shaida suna jira gwamnatin Jigawa da majalisar jihar su kawo, ko kuma su nemi hakkinsu a kotu kan bata musu suna.
Alhaji Kuit ya ce duk Najeriya babu inda aka yi aiki da gaskiya kamar Jihar Jigawa a zamanin tsohuwar gwamnatin ya ce ya je majalisar jihar amma babu inda aka same shi da laifin da ake tuhumarsu da shi. Saboda haka muddin gwamnati da majalisar jihar suka gaza gabatar da shaidar sun saci wadancan kudi ake cewa sun bata a hannunsu za su garzaya kotu kan bata musu suna.
Da ya juya kan gwamnatin APC, Alhaji Mamuda Kuit ya ce sun fuskanci APC ba za ta iya rike kasar nan ba, domin kowa ya ga gazawarta a fili, inda ya bai wa ’yan Najeriya tabbacin PDP za ta amshe mulkidaga hannun APC a cikin ruwan sanyi a zaben shekarar 2019.
Ya ce yana da tabbacin al’ummar Jihar Jigawa ba za su sake zabar Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ba, domin ya kasa cika alkawuran da ya dauka sannan jama’a suna fama da yunwa da fatara da matsi da kuncin rayuwa.