APC ba za ta iya warware rigingimunta nan da shekara biyu ba balle… Sanata Sodangi
Sanata Abubakar Danso Sodangi jigo ne a Jam’iyyar PDP, inda ya wakilce ta a Majalisar Dattawa sau uku a jere. Ya shaida wa Aminiya cewa sabuwar Jam’iyyar APC da wasu ke ganin barazana ce ga PDP ba za ta iya magance rigingimunta nan da shekara biyu ba, balle ta iya kada PDP a zaben badi: […]

Sanata Abubakar Danso Sodangi jigo ne a Jam’iyyar PDP, inda ya wakilce ta a Majalisar Dattawa sau uku a jere. Ya shaida wa Aminiya cewa sabuwar Jam’iyyar APC da wasu ke ganin barazana ce ga PDP ba za ta iya magance rigingimunta nan da shekara biyu ba, balle ta iya kada PDP a zaben badi:

Aminiya: Sanata jam’iyyarku ta PDP tana fama da matsalolin da suka shafi shugabanci, me kake ganin ke kawo wannan gutsuri-tsoma?
Sanata Sodangi: Maganar gutsiri-tsoma ko hayaniya ko hargitsi ko nuna son a sani da sauransu dole a same su, ba ma a jam’iyya mai girma irin tamu ta PDP ba. Kowace jam’iyya kai ko kungiya ce ta kasuwa ko ta ’yan dambe ko manoma, muddin za a samu mutum 100 ko 500, balle ana maganar miliyoyin da suke cikin Jam’iyyar PDP, dole a samu sabanin ra’ayi, shugabannin dole a dan jijjiga su a yi musu hayaniya wannan an gaje shi. Na biyu ko a kasashen da aka ce sun ci gaba irin su Amurka da Jamus da Kanada da sauransu duk wannan hayaniya ana yin ta, balle Najeriya yadda muka samu kanmu tun bayan samun mulkin kai aka yi zubin farko aka zo kan su Shagari da sauransu duk kamar koyo muke yi, domin dimokuradiyyar ta zauna da gindinta.
Amma saboda son zuciya na shugabanni, kowa na son in maganar neman mukami ne ya sa nasa ko shi ya shiga. Kamar yadda muka wayi gari a Najeriya cewa cin gajiyar dimokuradiyya sai wanda yake da mukami, ko jam’iyyar da ke kan mulki ko sai wanda ke cikin jam’iyya da ke kan mulki, wanda bai da mukami ba a yi da shi. Wannan ya kawo cin hanci da rashawa kowa ya shiga, zai kudunduna abin da zai kudunduna, wanda hakan ba abu ne mai kyau ba da ire-iren wadannan abubuwa su suke kawo hayaniya.
Mu koma maganar da kake yi ta jam’iyyarmu, ina nanata maka ba jam’iyyarmu ce kadai ke cikin wannan hayaniya ba, babu wata jam’iyya da ba ta cikin hargitsi ko hayaniya. Amma namu ya yi kamari ne ko an fi magana a kanta ce, saboda ita ce ja-gaba, ita ce ta daya. Ko mutum ya yarda ko kada ya yarda, PDP Allah Ya kawo ta ne kamar ruwan dare game duniya a 1999 aka rungume ta, muna da gwamnoni mafi yawa da rinjaye a Majalisar Tarayya da ta Dattawa da jihohi. To, a irin wannan hali dole ne a samu bambancin ra’ayi da son kai da sauransu.
Abu na biye lokacin da aka zabi Alhaji Bamanga a matsayin shugaban jam’iyya an samu ’yar hayaniya, kowa ya son wannan mukami, amma a karshe aka ce a bar wa Bamanga, shi aka zaba babu shakka da wasu da aka zabe su. Ka tuna Sakatarenmu Oyinlola har korarsa aka yi da aka ga irin tafiyarsa da yadda aka ga suke tangal-tangal.
Bugu da kari wasu suna ganin kamar zaman Bamanga Tukur a matsayin shugaban jam’iyya shi ne ake zaton kamar za a ba da takardar takara in Allah Ya kai mu shekarar 2015 ga Shugaba Jonathan. Alhali ga fahimtata ba haka ba ne, za a zo a yi zabe na share-fage za a zo a yi wasu abubuwa na ka’idojin da Hukumar INEC ko jam’iyyarmu su ne za a bi, wanda aka ga cancantarsa shi ne za a yi. To amma a yadda ni na karanci lamarin shi ne, ummulhaba’isin wadannan rigingimun ba wani abu ba ne, illa siyasa ce ta son zuciya. Da yawa wasu gwamnoni sun kudiri aniyar za su nemi wannan kujera ta Shugaban kasa. Suka samu Gwamna daya a Arewa, daya daga Kudu shi ne zai zama mataimakinsa. Aka fara kulle-kulle da bi-ta-da kulli da sauransu. Sannan na biyu wadannan gwamnoni za su bar kujerarsu saboda suna zangonsu na biyu, sai suka ga in suka tsaya a PDP, yadda suka fara tangal-tangal shin PDP za ta goya musu baya kan wadanda suke so su nada don rufa musu asiri kada ya yi musu fallasa, sai suka ga kamar ba za su samu haka ba, shi ne suka zamo ’yan tawaye, ’yan sabuwar PDP, alhali ba a taba yin haka ba. Kana cikin jam’iyya ka ce ka fita daga cikinta, kuma ana cikin taro na kasa ka fice, ai ko kawaici da irin al’adunmu na Afirka ba su lamunci haka ba, sai mutum ya zauna a gida ya ki zuwa Abujan tun farko. Amma ka zo Abuja ka dauki rigar PDP ka zo taro, Shugaban kasa da kowa na wurin, gwamnoni ’yan uwanku na wurin ko don karamcin wadannan mutane a bari, amma suka fallashi kansu suka fada wa duniya su kamar ’yan tawaye ne suka balle.
Ina kalubalantar duk wanda ya karanta wannan jarida a cikin gwamnonin da suka yi tawayen wane ne ba ya da wata manufa na abin da yake so ya kare wa kansa? Son zuciya ne da son kai da son kowa ya kare abin da yake so suka sa aka manta da ka’idojin bi na siyasa.
Aminiya: In na fahimce ka kana nufin son zuciyar daidaikun ’yan jam’iyyar ne ya kawo rikicin PDP?
Sanata Sodangi: kwarai kuwa, son zuciya da son kai ne. Bayan son zuciya akwai rashin bin ka’ida da rashin ladabtarwa da aka saba da shi. A matsayina na lauya duk wata kungiya ko ta mece ce, koda ta ’yan dako ce, in ka shiga akwai ka’idoji ga abin da za ka yi don bin dokar wannan kungiya tamu, haka jam’iyya tana da wadannan ka’idojin da aka shimfida. A nan Najeriya na lura akasarin mutane, musamman wadanda suke bangaren mulki na zartarwa, gwamnoni da Shugaban kasa da ciyaman muddin suna da wuka da nama sukan taka dokokin da aka shimfida. Ko domin su suke ba da kudi na gudanar da jam’iyyar ko suke da ’yan majalisa da za su sa a cire ko a bakanta mutum ko a kuntata masa. Mun wayi gari wasu gwamnonin ma suna da irin ’yan ta’addansu ko yara da sukan diba a bata mutane. A baci mutum a gidan jarida ko rediyo ko talabijin a same ka a wurin biki a bace ka. To, duk wannan rashin ladabi ne da rashin bin ka’idar jam’iyya.
Aminiya: Ba ka ganin tun farko jam’iyyun ba a gina su kan ka’ida ba, inda za a nuna shugaban jam’iyya na sama da zababbe, ba ka ganin wannan ne ya kawo haka?
Sanata Sodangi: Gaskiya haka ne, yadda jam’iyyun suka ta so a 1999 ba zan koma can baya ba, amma ko a Jamhuriyya ta Biyu jam’iyyun da aka kafa babu wannan hayaniya. Lokacin NPN, Cif Akinloye ne shugaban na kasa, ba Shehu Shagari ba. Shagari shugaba ne wanda aka zaba shi kansa yana karkashin Akinloye ne, haka kowace jiha shugaban jam’iyya shi ne shugabanta a jiha ba gwamnonin da aka zaba ba, haka a karamar hukuma har unguwanni. Amma aka wayi gari a 1999 sojojin da ake maza-maza a kawar da su, tsarin mulkinmu ma haka aka kudunduna shi a gurguje aka mika mana. To lokacin da ake son sojoji su tafi lokacin Abacha jam’iyyun siyasar kasar nan sun tsayar da shi ne a matsayin dan takararsu, Abdulsalami cikin shekara daya ya kudiri aniyar mika mulki shi ne aka kafa PDP da APP da AD kowacce ta yi tsari ta zabi shugabanninta. To, amma da aka shigo Obasanjo ya zama Shugaban kasa, sai ya dauki su Solomon Lar su Gemade su Audu Ogbe da su Ahmadu Ali, komai za su yi sai sun je sun durkusa a gaban Obasanjo sun ce Sa. Don me? Shi ke gudanar da jam’iyya, shi ke ba ta kudi, shi ke ba da duk abin da ake tafiyar da jam’iyya sai abin da ya ce. Haka a jihohi gwamnoni suka maida abin, su ne wuka su ne nama. Wannan ne rauni da kasawar da aka samu a siyasa, aka manta da tsarin yadda ake yi a duniya. Aka manta shugaban jam’iyya ne zai yi wa Shugaban kasa tsawa, na jiha ya yi wa gwamna tsawa ya tabbatar ba a samun sabanin a tsakanin Shugaban kasa da ’yan majalisar ba, haka gwamna da ’yan majalisar jiha har a matakin karamar hukuma, ya ce ga abin da tsarin jam’iyyarmu ya kunsa na abin da za ta yi wa jama’a. Saboda kwadayin abin duniya sai aka watsar da wannan, sai a ce sai abin da zababben shugaba ya fadi. Wannan ya kawo rashin ladabi a jam’iyyun da rashin samar musu da kudi kamar yadda ake yi a duniya, inda ake yin gidauniya a ajiye wa jam’iyya kudin gudanar da ayyukanta ba zababbun shugabanni su rika ba ta kudi daga asusun gwamnati ba.
Aminiya: Ta wace hanya za a gyara wannan matsala?
Sanata Sodangi: Hanyar da za a bi a gyara, na daya in za a yi zabe misali na shugaban jam’iyya na kasa, a bar ’yan jam’iyya su zo da wakilansu da aka tsara, mutane dari-dari ne ko hamsin-hamsin ne. Kuma a yarda jama’a su zabi wanda suke so, ba wanda Shugaban kasa yake so ba. Su kuma in an zabe su, su yi mulkin tsakaninsu da Allah, ba sai in za a yi zabe da ya shafi na cikin gida wadanda suka kai wa shugabannin kudi ne za su ba su takardun tsayawa takara ba. Domin wasu da yawa sukan manta da cancanta sai wane ne ubangida ko uwargijiyar dan takara ko shi dan wane ne ko me zai kawo mana, wannan dole sai an kawar da shi. Abu na gaba shugabannin da aka zaba a can sama da suke duba yadda ake al’amura su bar kawo kudin da suka tara ko ta wane hali su ba shugabannin don su zabi su yi abin da ba daidai ba. Idan aka yi wadannan abubuwa insha Allahu ina ganin za a gyara tafiyarmu ba ma na jam’iyya kadai ba, har mulkin kasar. Mutum zai zo da tsoron Allah ba don kudin da ya bayar ba, ba don ubangidansa ba, saboda duk wanda aka zabe shi hakki ne a kansa ya san cewa Allah zai tambaye su gobe kiyama. Don haka duk wani mai son neman mukami saboda wani abin duniya da kwadayin tara abin duniya ba zai yi haka ba.
Aminiya: Kana ganin saukar Bamanga za ta sa PDP ta warware rikicinta?
Sanata Sodangi: Eh, a’a. Na ce eh, a’a ne saboda wadanda suke zargin shi ne karen farautar Shugaba Jonathan a lokacin zabe ko wani ko wasu, to ya tafi. In suna tsammanin idan Bamanga ya tafi shi ne za su samu nasu damar ta cimma bukatun kashin kai. Kamar yadda na fadi galibin ’yan siyasa muna da bukatu na kashin kai, me zan samu? Yaya zan yaudari wane, ko ’yan jam’iyyarmu ni in samu abin da nake so? To ya tafi, saura da me wadanda suka yi gudun hijrar nan sai su dawo. Amma ina tabbatar maka ba za su dawo ba, tafiya ta yi nisa, shi ya sa aka ce mutum ya daina saurin yanke hukunci. Yanzu kamar an kalubalance su ne gwamna wane dan majalisa wane, masu cewa sai Tukur ya tafi, to Tukur ya tafi sai ku dawo. Ba za su iya dawowa ba, munafuncin ne saboda wannan kullalliya na suna son zama Shugaban kasa, suna son tafiya Majalisar Tarayya suna son kaza da kaza, suna tsammanin in suka je suka yi wannan hadin-gambiza ne za su samu nasara ba Tukur ba ne. Ka ga ashe tafiyar Tukur ba ita ba ce gare su. Kuma wadanda suka matsa sai Tukur ya tafi sun yi fargar jaji. Wadancan gwamnoni sun tafi, Tukur ya tafi to me aka yi? Gwamnonin da suka tafi ba za su dawo ba. Ina tabbatar maka wadanda za su rufe idonsu su dawo su ce don Allah PDP Tukur ya tafi mun dawo, za a karbe su amma da tunanin jemagu, wadanda suka gudu suka dawo. Idan suka zauna can kuma ina tabbatar maka galibinsu ba su yi abin kirki ba, ba su zuwa garuruwansu ba su tare da mutanensu sun zama ’yan Abuja. Akwai wadanda nake girmamawa a cikin gwamnonin ba zan ambaci suna ba, saboda suna yin abin da ya dace.
Cigaba a shafi na 27
Amma tunaninsu shi ne idan muka tsaya wannan mai malfar ba zai yarda mu samu shugabancin da muke so mu dana ba, Arewa za ta cutu da sauransu.
Ina tambayarsu, su wa suka kawo mana Obasanjo? Su gaya mana ’yan Kudun da suka tara kudi suka yi amfani da ilimi da hankalinsu suka ce ga Obasanjo, a fito da shi daga gidan kurkuku yana hargagin zaman kurkuku a ba shi mulki. Suka ce ya je ya yi. Kuma ya yi ta bundun-bundun dinsa lokacin duk abin da ya yi sai a ce muna koya ne. Ya yi ta fada da mu ’yan majalisa ya yi fada da wancan, ya ce mu yi hakuri, yana amfani da hankalinsa na soja wai muna koya ne don dimokuradiyya ta zauna da gindinta. Ya shekara hudu, Atiku dan dimokuradiyya ya fito aka yi masa ca aka ce ya bar masa ya shekara takwas. Kuma wane ne umulhaba’isin kafa mana Jonathan ba Obasanjon ba ne da hadin bakin ’yan Arewa? Yanzu sun zo suna ce mana ba sa son Jonathan, suna yin haka ne domin suna son mulkin kawai.
Aminiya: Akwai masu ganin Jam’iyyar APC barazana ce ga Jam’iyyar PDP, a matsayinka na dan jam’iyyar me za ka ce?
Sanata Sodangi: Har ka ba ni dariya, babu wata barazana da Jam’iyyar APC take yi wa PDP. Da suna yi tsakaninsu da Allah ne da sai in yi ta Fulani in ce mun shiga bone, mun shiga uku mun lalace, da sai in ce lallai za mu ji jiki mu PDP. Kuma sai in ce za a yi kare jini biri jini, ba fa na fada ba, a zabe mai zuwa. A ga wadda ’yan Najeriya za su zabe ta, wane ne ke kamanta tsoron Allah, kai Musulmi ne ko Kirista wace jam’iyya ce take da cikakkiyyar takardar da ta tsara na wani ra’ayi irin na gurguzu ne ko jari-hujja. Babu! In kuwa haka ne APC hadin gambiza ne da girmamawa gare su. APP da ta zama ANPP da AD da ta zama AC ta zama ACN da CPC ne suka hadu suka kafa APC. Ba hadewar ba ce, babban kalubalen da ke tare da APC shi ne shugabancin ma tun daga tushe wato unguwanni ba su da shugabannin da za su ce an zabe su ne. A ce jama’a sun ce a unguwar nan tamu mun san wane mai tsoron Allah ne ko su wane za su rike mana amana a jam’iyya mun zabe su shugabance ta. Ba su da shi, a kananan hukumomi babu, a shiyyoyin mazabar Sanata bau, jihohin nan 36 babu, babu a matakin shiyyoyi shida na siyasar kasar nan balle a matakin tarayya. In aka ce akwai rikon kwarya babbar illa ke nan, domin in dimokuradiyyar suke tsakani da Allah ne yadda suke gaggawar bin tsofaffin ’yan siyasa suke ta kai da dawowa don kama su, me ya sa ba za su yi gaggawar zaben shugabannin jam’iyya a dimokuradiance cikin mako daya ko wata daya akalla cikin wata uku su kafa harsashin jam’iyyar ba? Ba su yi ba, sai kawai ana nade-nade, to a nade naden nan ne za a samu illa ga tafiyar jam’iar da siyasar Najeriya. Rikicin da ke cikin APC ya fi na PDP. Muna sane da batun da ya taso cewa duk gwamnan da ya koma APC shi ne jagora a jiharsa, kamar Sakkawato da Kano da Adamawa da Kwara su biyar din nan. Abin bakin ciki gare su a Sakkwato akwai Bafarawa wanda shi ne ginshikin kafa APP da ya zama ANPP, kuma ko mutum bai so, bai cewa Bafarawa bai da iya cewa a wannan hadin gambiza da aka yi, su ne kanwa uwar gamin hadewar a je Legas wurin Tinubu a kai a dawo, ka zo ka ce yanzu ya koma wurin wanda kusan ba su ga maciji wato Wamakko sai abin da ya ce masa. Yau ba gobe ba, akwai ofishin bangarorin jam’iyyar guda biyu a Sakkwato ga na Bafarawa da ake cewa shi ne APC na asali ga na Wamakko. In ka je Kano da Kwankwaso da Malam Shekarau suna nan sun raba gari su da magoya bayansu. In ka je Adamawa Buba Marwa da Gunduri da ya yi takara da Baba Mai Mangoro suka yi kusan kankankan, a gefe guda sun raba gari da Nyako.
To wadannan yaushe za su zo su kafa shugabanninsu, su tunkari PDP wadda kowace unguwa zuwa kananan hukumomi 774 da jihohi 36 da tarayya muna da shugabanni? Yanzu muna tunanin yaya za mu je mu tunkari jama’a mu ce ga nasarorin da muka samu a tarayya da jihohi ga abin da muke so mu yi muku a baayn zabe mai zuwa. Wadannan na APC suna can suna kalubalantar junansu suna caccakar junansu wannan yana bata wancan, wancan yana bata wannan, yaushe suka sasanta balle har su tunkari PDP a zabe? Ina tabbatar maka nan da shekara daya ko shekara biyu ba za su iya sasantawa ko su magance rikicinsu ba, balle su kada PDP a zaben. Kamar annoba ce babba ta fada wa APC da wadannan da suka guje mana suka fada cikinta, don dama muna alla-alla yaya za mu rabu da su ne sai suka koma can suka same su. Don haka mun san muna tare da jama’a ba wata barazana da APC ake yi ga PDP, muna tare da nasara. Wannan hayaniya da ake yi a PDP mun saba ganin haka a duk lokacin da zabe ya karato, kuma insha Allah za mu magance mu samu nasara a zabe mai zuwa.