APC ba za ta zama barazana ga PDP a Jihar Kano ba -Musa M. Musa
Dokta Musa M. Musa na hannun damar tsohon Shugaban Majalisar Tarayya Ghali Umar Na’abba ne, a tattaunawarsu da Aminiya ya ce Jam’iyyar APC ba ta girgiza karfin Jam’iyyar PDP a Jihar Kano ba. Ya kuma tabo tabarbarewar alakar siyasa tsakanin Kwankwaso da Na’abba: Aminiya: A kwanan nan an ji Alhaji Ghali Na’abba a wata kafar […]
Dokta Musa M. Musa na hannun damar tsohon Shugaban Majalisar Tarayya Ghali Umar Na’abba ne, a tattaunawarsu da Aminiya ya ce Jam’iyyar APC ba ta girgiza karfin Jam’iyyar PDP a Jihar Kano ba. Ya kuma tabo tabarbarewar alakar siyasa tsakanin Kwankwaso da Na’abba:
Aminiya: A kwanan nan an ji Alhaji Ghali Na’abba a wata kafar labarai ya yi wasu kalamai da ba su yi wa bangaren Kwankwasiyya da ke mulkin jihar dadi ba, me za ka ce a kan hakan?
Dokta Musa: Alhaji Ghali mutum ne da ba ya boye abin da ke zuciyarsa. Kalaman da ya fadi a gidan rediyo abubuwa ne da suka faru, sai dai mu ce ya fade su a wurin da ya fi karfin tunanin magoya baya, wadanda ke yi wa maganganun wani irin kallo. Gwamna Kwankwaso shi ya jawo maganganun suka kai ga haka, dubi da irin karfin dangantakar da ke tsakanin mutanen biyu. Ba na mancewa a lokacin yakin neman zaben Kwankwaso, Ghali ya tsaya tsayin daka da karfinsa da dukiyarsa da jama’arsa aka yi yakin neman zabe har aka kai ga nasara. Duk wani abu na daukaka PDP a Jihar Kano da Ghali aka yi. Amma saboda irin yanayin siyasa ta jihar sai wasu mutane da ba sa kaunar zaman lafiya wadanda suke ganin idan kyakkyawar dangatakar da ke tsakanin mutanen biyu ta karfafa ba za su samu tasu biyan bukatar ba, don haka suka shiga suka fita sai da suka cimma burinsu. Wannan ya haifar da baraka a tsakaninsu har abin da ya faru ko yake faruwa a yanzu. Wani abu da mutane ba su sani ba, shi ne har yanzu ’yan PDP sukan je wurin Ghali da jar hularsu a kansu, kuma shi bai taba cewa su cire hular ba. Ka ga wannan yana tabbatar da cewa ba wai Kwankwason yake ki ba, sai dai wasu abubuwa da suke faruwa.
Aminiya: Ana ganin batun raba arzikin fetur na tudu da teku (onshore da offshore) ne ummal’abisin rura wutar rikici a tsakanin mutanen biyu, mene ne gaskiyar lamarin?
Dokta Musa: Gaskiya ne batun raba tattalin arzikin kasa na onshore da offshore shi ya kara rura wutar rikici a tsakaninsu. Shi man fetur akwai wanda ke samu a tudu akwai wanda ake samu a ruwa kasancewar batu ne wanda zai kara ba wani bangare dama tare da danne wani bangare na kasar ya sa aka yi ta tattauna shi a majalisa, inda Ghali a lokacin yana rike da shugabancin majalisar suka yi iya kokarinsu don ganin wanann batu bai tabbata ba. Amma saboda sha’ani na siyasa a lokacin shugabancin (Aminu) Masari, (Cif) Obasanjo ya yi nasarar tabbatar da batun a matsayin doka. Amma sai gashi daga baya Gwamna Kwankwaso ko bai nazarci abin ba, ko kuma zugar jama’a ce ko tunaninsa ne, sai kawai ya shiga kafafen watsa labarai ya ce a lokacin Ghali ne aka zartar da wannan batu. Wanda kuma ba haka ba ne. Wannan babatu da ya zo ya yi shi ya tunzura Ghali har ya taimaka wajen kara tabarbarewar mu’amalarsu, domin ba Ghali kadai maganar ta yi wa ciwo ba, har da sauran ’yan majalisar wadanda suka tsaya ba dare ba rana wajen ganin sun jingine dokar.
Aminiya: Yaya kake ganin tsarin tafiyar da aikace-aikacen gwamnatin PDP a Jihar Kano a yanzu?
Dokta Musa: Babu shakka tsarin tafiyar da gwamnati a Jihar Kano abin a yaba ne, lura da irin dimbin aikace-aikacen da gwamnati ke yi. dauki batun daukar nauyin daliban jihar don yin karatu a kasashen waje da kuma makarantun da aka bubbude a jihar. Haka kuma idan aka koma batun tituna an samu nasara ba karama ba, domin ko’ina ka bi a jihar za ka ga tituna masu kyau kuma manya. Idan aka dauki Hukumar Hisba yadda ta fito da sababbin shirye-shirye masu kyau da magani ga jama’a wannan ma ci gaba ne. Babu shakka mu ‘yan PDP muna jin dadin wannan aikace-aikace, domin mun san nasarar ta jam’iyyarmu ce. Muna fatan idan wata gwamnatin tamu ta zo a nan gaba ta dora a kan wadannan kyawawan ayyuka.
Aminiya: Har yanzu akwai korafe-korafe daga jama’a game da yadda gwamnatin ke aiwatar da wasu al’amura wane jan hankali za ka mata?
Dokta Musa: Babu shakka akwai irin hakan, domin idan aka dauki sojojin baka wadanda su ne suka tallata jam’iyyar da shi kansa Gwamna ta yin amfani da kudadensu a kafafen watsa labarai, amma an bar su a gefe, babu wanda aka yi wa wani abin a zo a gani. Mutanen nan su ne suka haska Gwamnan ta hanyar zakulo abubuwa na alheri suna gaya wa jama’a har aka kai ga nasara. Idan ni zan iya yin magana da mutum daya a game da wani lamari, wanda ya shiga kafar watsa labarai yana magana ne da dubban mutane wanda hakan yake tasiri a wajen masu sauraro. Ni har tsoro nake kada mutanen nan su balle daga gwamnati, domin idan aka yi haka to fa gwamnatin kasa za ta yi. Haka kuma banagaren ayyukan KAROTA duk da cewa suna aiki sosai domin zuwansu ya magance matsalar cinkoso a tituna da sauransu, sai dai suna bukatar a seta su yadda ayyukansu za su dace da zamani.
Aminiya: ’Yan adawa na ganin cewa tsoron faduwa a zabe ya hana gwamnatin PDP shirya zaben kananan hukumomi a jihar, mene ne gaskiyar wannan batu?
Dokta Musa: Wannan magana ba haka take ba, duk da cewa mu kanmu ba mu san dalilin da ya sa Mai girma Gwamna ya hana aiwatar da zaben kananan hukumomi a jihar ba. Ya kamata a ce gwamnatin Jihar Knao ta gaggauta yin zaben kanann hukumomi, domin al’ummar wadanan kananan hukumomi su fara amfanar ko jin romon dimokuradiyya. Babu shakka a tafiyar da ake yi yanzu na kantomomi talaka ba zai fahimci me ake so a aiwatar na ci gaban dimokuradiyya a yankinsa ba. Amma yayin da aka ce an samu shugabannin kanana hukumomi da kansiloli ka ga an kafa kyakkyawar dimokuradiyya a karkashin karamar hukuma. Ban san dalilin da ya sa Gwaman da mashawartarsa suka kasa fahimtar da mu dalilinsu na kin gudanar da zaben kananan hukumomin ba. Idan dai ana so a kafa dimokuradiyya a Jihar Kano sosai, to, ya kamata a yi zaben nan. Dama ba za mu iya cewa za mu ci zabe a dukkan kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar ba, amma na san za mu samu kaso mafi tsoka a ciki. Ina kira da Gwaman ya gaggauta gudanar da zaben, domin daga nan ne za mu kara tabbatar da karfinmu a jihar.
Aminiya: Yaya kake hangen nasarar jam’iyyarku ta PDP a Jihar Kano a zaben 2015, lura da bullowar sabuwar Jam’iyyar APC?
Dokta Musa: Jam’iyyar PDP uwa ce kuma rumfa ce, don haka babu wata jam’iyya daya ko biyu zuwa uku da za su hada kai su zame mata barazana. Su mutanne Kano suna la’akari ne da abin da mutum ya yi na amfanar jama’a, idan aka duba gwamnatin baya ta ANPP ta shigo da farin jininta amma da ba su yi wani abin kirki ba, ai PDP ce ta dawo ta karbe mulkin, dama wajenta ne. Babu wata jam’iyya da za ta samu hadin kan da za ta iya rusa karfin PDP a Jihar Kano da kuma kasa baki daya. Irin ayyukan alherin da gwamnatin ke yi a Jihar Kano ya kara jawo wa jam’iyya farin jini, inda a kullum sai shiga cikin jam’iyyar suke yi, don haka muna sa ran cin zabubbukanmu gaba daya a Jihar Kano ba tare da shakku ba.