APC ce za ta kafa gwamnati a badi – Musan Sati
Alhaji Bashir Musan Sati shi ne ya lashe zaben Sakataren Jam’iyyar APC reshen Jihar Filato. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce Jam’iyyar APC ce za ta kafa gwamnati a zaben mai zuwa, kuma ya musanta maganganun da wasu suke yi cewa jam’iyyar ba za ta samu karbuwa a Jihar Filato ba. Aminiya: Yaya ka ga […]
Alhaji Bashir Musan Sati shi ne ya lashe zaben Sakataren Jam’iyyar APC reshen Jihar Filato. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce Jam’iyyar APC ce za ta kafa gwamnati a zaben mai zuwa, kuma ya musanta maganganun da wasu suke yi cewa jam’iyyar ba za ta samu karbuwa a Jihar Filato ba.
Aminiya: Yaya ka ga yadda zaben sababbin shugabannin Jam’iyyar APC reshen Jihar Filato ya gudana?
Musan Sati: To, zabe dai an riga an yi ya wuce. Babu shakka a lokacin zaben mun ga abubuwa da dama, to amma duk da haka Allah Ya taimake mu mun kammala lafiya.
Aminiya: Me za ka ce kan maganganun da wasu suke yi cewa Jam’iyyar APC ba za ta samu karbuwa ba a nan Jihar Filato, musamman ganin yadda al’ummar jihar suka rungumi Jam’iyyar PDP?
Musan Sati: Wannan magana ce kawai, Allah Ya kai mu lokacin zabe jama’a za su yi mamakin ganin yadda wannan jam’iyya za ta mamaye wannan jiha. Domin mutane suna ta rububin shiga jam’iyyar a nan
jihar. Idan da wannan jam’iyya ba za ta samu karbuwa ba, ai da a wajen zaben shugabannin da muka yi, ba za a ga jama’a ba. Kai kanka ka ga irin dimbin mutanen da suka halarci wajen wannan zabe. A lokacin
zaben duk kananan hukumomi jihar 17 babu karamar hukumar da wakilanta ba su zo ba, haka kuma babu karamar hukumar da wakilanta ba su nemi takara ba. A da ne mutanen Jihar Filato suki dauki Jam’iyyar PDP da wani kima, amma yanzu karshen PDP yazo a Jihar Filato don kowa gudunta yake
yi a jihar.
Aminiya: A matsayinku na shugabannin wannan jam’iyya a nan jihar, wadanne shirye-shirye za ku yi don ganin kun yada jam’iyyar?
Musan Sati: Da farko ina son a gane cewa duk lokacin da aka ce a jam’iyya akwai zaben ’yan takara, dole za a samu gutsiri-tsoma nan da can. Saboda haka abin da muke fata shi ne a yanzu za mu yi kokari mu
warware wadannan abubuwa baki daya. Idan muka warware su, sai mu manta da abubuwan da suka faru a baya mu hada kanmu mu kara fadakar da mutanen jihar nan manufofin wannan jam’iyya. Saboda
haka ina tabbatar maka cewa wannan jam’iyya tana da kyakyawan nufi ga al’ummar Jihar Filato da kasar nan baki daya.
Aminiya: Wasu suna maganganu cewa rikice rikicen da suke faruwa a wasu jihohin kasar nan, zai iya kawo wa wannan jam’iyya cikas a zaben badi, me za ka ce?
Musan Sati: Babu jam’iyyar da za ka ce ba ta fuskantar irin wadannan rikice-rikice a Najeriya da kasa baki daya. Kuma duk rikice-rikicen da suke faruwa a Jam’iyyar APC ba rikice-rikice ne da za su hana a hadu a yi wa kasa aiki ba. Kuma kamar yadda kake ganin mutane daban-daban haka ra’ayoyinsu suke daban-daban. Don haka ina tabbatar maka wadannan abubuwa da kake gani a jam’iyyarmu abubuwa ne da za su kara mana karfin gwiwa.
Aminiya: Wato akwai alamun jam’iyyarku ta APC za ta iya kafa gwamnati a Najeriya?
Musan Sati: Babu shakka da yardar Allah mutanen kasar nan za su zabi APC ta kafa gwamnati a Najeriya. Ina tabbatar maka cewa in Allah ya yarda gwamnatin da za a yi a Najeriya a zaben badi gwamnatin APC ce. Wadda za ta yi wa mutanen Najeriya adalci ta kawo masu walwala.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga al’ummar kasar nan?
Musan Sati: Kirana ga al’ummar Najeriya shi ne kowa ya kwantar da hankalinsa ya kawo gudunmawarsa mu taru mu canja miyagun abubuwan da suke faruwa a kasar nan.