APC da PDP na rikici a kan gyaran masallaci
’Ya’yan jam’iyyun APC da PDP na rikici a kan gyaran babban masallacin unguwar Sabo da ke birnin Ibadan, inda daukar nauyin aikin ya haifar da wata hatsaniya a tsakanin magoya bayan wadannan jam’iyu ranar Talatar da ta wuce. Dattijan gari ne suka hanzarta daukar matakin shawo kan al’amarin kafin ya kazance. A wani bincike da […]
’Ya’yan jam’iyyun APC da PDP na rikici a kan gyaran babban masallacin unguwar Sabo da ke birnin Ibadan, inda daukar nauyin aikin ya haifar da wata hatsaniya a tsakanin magoya bayan wadannan jam’iyu ranar Talatar da ta wuce. Dattijan gari ne suka hanzarta daukar matakin shawo kan al’amarin kafin ya kazance.
A wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa, a kwanan baya ne Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, wanda shi ne dan takarar kujerar gwamna a karkashin Jam’iyar APC a zabe mai zuwa ya yi alkawarin yin kwaskwarima ga babban masallacin na Sabo sai dai bai iya gudanar da wannan aiki a wancan lokaci ba, sai a ranar Talata da wasu matasa suka hana ma’aikata yin wannan aiki. Dalilin hana yin aikin da wadannan gungun matasa suka bayar shi ne, bai kamata wani ya zo ya ce zai yi aikin gyaran masallacin a daidai lokacin da dan takarar gwamna na Jam’iyar PDP a Jihar Oyo Sanata Teslim Folarin, ya riga ya fara gudanar da aikin shafen fenti na bangwayen ciki da wajen masallacin ba.
Uwargidan Sanata Teslim Folarin ita ce ta fara ziyartar harabar masallacin a wannan rana daga baya kuma mijin na ta ya kai irin wannan ziyara zuwa fadar Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ahmad dahiru Zungeru, a inda ya yi wa al’ummar Hausawan alkawarin biya musu bukatun rayuwa idan suka zabi PDP a zabe mai zuwa. Sai dai jim kadan bayan ficewarsu daga fadar Sarki ne wasu magoya bayan PDP bangaren Hausawa suka fara zargin wasu fadawa da yin awon gaba da dimbin kudin da Sanata Folarin ya bayar domin a raba wa jama’a.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Shugaban Jam’iyyar PDP na mazaba ta shida a birnin Ibadan, Alhaji Bala Abdulkadir Jada, cewa ya yi “a ranar Larabar makon jiya ne muka nemi Sanata Teslim Folarin da ya taimaka yayi wa babban masallacinmu shafen fenti wanda a nan take ya amince. Amma a daidai lokacin da muka fara gudanar da wannan aiki sai wani yaro mai suna danladi da yake wakiltar Gwamna Abiola Ajimobi a wannan mazaba ya shigo da ma’aikata da suka fara aikin cire tagogi da kofofin masallacin, amma al’ummar gari baki daya suka nuna kyamarsu ga wannan aiki, wanda ba a nemi izinin yin hakan daga Sarkin Hausawa da Shugabannin kwamitin masallacin ba. Saboda haka a nan take suka hana su ci gaba da yin aikin. Yau watanni takwas da suka wuce ke nan da Gwamna Ajimobi ya yi alkawarin gyaran wannan masallaci, amma ya kasa cika alkawarinsa sai yanzu da suka ga mun fara yin namu aikin cikin dan lokaci kadan shi ne suka yunkuro domin tsokanar fada.”
Shi kuwa Shugaban bangaren Hausawa na Jam’iyar APC a Jihar Oyo, Alhaji danladi Garba cewa ya yi, “gaskiya ne a wani lokaci da ya gabata Gwamna Abiola Ajimobi ya yi alkawrin gudanar da aikin kwaskwarima ga wannan masallaci, amma Allah (TWT) bai ba shi ikon cika alkawarin ba sai a makon jiya da ya bayar da umarni. Amma a lokacin da muka zo domin gudanar da aikin sai muka taras da magoya bayan PDP suna aikin shafen fenti a jikin bangwayen masallacin, muka yanke shawarar yin hakuri zuwa ranar Talata da safe da suka kammala aikinsu.
Da muka kawo ma’aikata da kayan aiki domin yin ayyukan gyaran kwanukan rufi da tagogi da kofofi da sumuntin tayil da shimfidun masallaci da na’urar sauti (lasifika), muna cikin tattaunawa da kwamitin masallaci sai muka ji isowar matar Teslim Folarin da hayaniyar mutane cewa ba za mu yi aikin na mu ba,” inji shi.
A cewarsa: “Wannan abu ya ba mu mamaki, musamman saboda ganin cewa, masallaci dakin Allah ne da kowane musulmi zai iya bayar da gudunmawar gyaransa. Amma a dalilin tsoma bakin dattijai ne muka hakura zuwa wani lokaci a nan gaba.”
Dangane da zargin karbar kudi Naira miliyan biyar na gyaran wannan masallaci da ake cewa, Kakakin majalisar dokoki ta tarayya Aminu Waziri Tambuwal, ya bayar a lokacin wata ziyara da ya kai zuwa unguwar Sabo tare da Gwamna Ajimobi a kwanan baya, sai Alhaji danladi Garba ya yi rantsuwa.
“Wallahi Tallahi ba bu kamshin gaskiya a cikin wannan magana. Lokaci ne na siyasa da suka yi amfani da shi domin su bata sunanmu. Idan mu ba mu dauki kudin aljihunmu mun gyara dakin Allah ba to, kuwa babu yadda za mu yi rubda ciki da kudin da aka bayar ta hannunmu domin gyaran dakin Allah. Kamata ya yi masu fadin haka su yi binciken kwakwaf a kan wannan al’amari domin bai kamata su rika yin amfani da addini domin bata sunayen ‘yan uwansu ba.” Inji shi.