APC da PDP na takaddama kan zaben kananan hukumomin Katsina

Jam’iyyar APC reshen Jihar Katsina ta zargi gwamnatin jihar da ba wasu daga cikin ’yan takarar shugabannin kananan hukumomin da suka fito daga Jam’iyar PDP a zaben 6 ga Satumb damar ci gaba da mulkin kananan hukumomin tare da jami’an da ke rikon kananan hukumomin tun kafin a yi zabe. Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar […]

APC da PDP na takaddama kan zaben kananan hukumomin Katsina
APC da PDP na takaddama kan zaben kananan hukumomin Katsina

Jam’iyyar APC reshen Jihar Katsina ta zargi gwamnatin jihar da ba wasu daga cikin ’yan takarar shugabannin kananan hukumomin da suka fito daga Jam’iyar PDP a zaben 6 ga Satumb damar ci gaba da mulkin kananan hukumomin tare da jami’an da ke rikon kananan hukumomin tun kafin a yi zabe. Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Dokta Mustafa Inuwa ya yi wannan zargin a ranar Talata a wajen
taron manema labarai da jam’iyyar ta kira inda ya ce, “Wadannan mutane da aka ce an tsai da ’yan takara a yanzu su suke yin aikin ciyamomi a kananan hukumomi. Akwai kananan hukumomin da mutanan nan har ofis suke zuwa suna yin aiki, suna sa hannu cewa a kashe kudi kaza ko a yi kaza.”
Dokta Inuwa ya ce, wannan ya saba wa hankali da duk wata doka a kasar nan. “In yana so ya nada su riko mana kawai. Amma a ce dan takara ya je ofis ya kama kuma a ce wai zabe ake so a yi,” bai dace ba inji shi.
Sai dai a martanin Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Katsina Alhaji Rabi’u Gambo Bakori kan zargin na APC ya ce, mutanen Katsina ba mahaukata ba ne, domin ba zai yiwu a ce daga tsayar da mutum takara ya zo ya kama kashe kudin karamar hukuma ba.
Alhaji Rabi’u Gambo ya ce, suna kallon irin wannan a siyasance a matsayin soki burutsu ne na wata jam’iyyar da ba ta da jama’a. “Su yi kokari su magance rikicinsu na cikin gida. Ana cewa jam’iyyar adawa, wannan ba jam’iyyar adawa ba ce, kungiya ce ta mahassada,” inji Gambo Bakori.