APC da PDP sun saka Wike a kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Bayelsa

Da alama Ministan na Abuja ya yi kasuwa a jam’iyyun

APC da PDP sun saka Wike a kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Bayelsa

Da alama Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi kasuwa inda jam’iyyun APC da PDP suka sanya sunan shi a kwamitocinsu na yakin neman zaben Gwamna a Jihar Bayelsa.

Za a yi zaben Gwamna a Jihar ce a ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Tsohon Karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva ne dai yake yi wa jam’iyyar APC takarar, yayin da Gwamna mai ci, Douye Diri, ya tsaya wa PDP.

A cikin sunayen da Sakataren Tsare-tsaren na APC na kasa, Suleiman Muhammad Argungu, ya fitar ranar Talata, APC ta sanya sunan Wike da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da sauran masu rike da mukaman siyasa.

Jam’iyyar ta kuma sanya sunan Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya a matsayin shugaban kwamitin.

Sai dai tun gabanin nan, a farkon watan nan jam’iyyar PDP ta kaddamar da kwamitin yakin neman zabe mai mambobi 72, wanda Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas ke jagoranta, shi ma da sunan Wike a ciki.

Sai dai a lokacin Wike bai halarci kaddamar da kwamitin kamfen din na PDP ba.

Wike dai ya shafe shekara takwas a matsayin Gwamnan Jihar Ribas a karkashin jam’iyyar PDP, kodayake ana gani shi da wasu Gwamnoni hudu da suka yi wa kansu lakabi da G-5 sun taka muhimmiyar rawa wajen faduwar jam’iyyar a zaben Shugaban Kasar da ya gabata.

Daga bisani Shugaban Kasa Bola Tinubu ya saka masa da mukamin na Ministan Abuja, duk da yana cikin PDP.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan