Kwankwaso kadai ba zai iya kai TNM gaci ba —Dokta Dukawa
Dokta Dukawa ya ce Kwankwaso ba shi da nauyin da zai yi abin da Obasanjo ya kasa
Tun bayan kaddamar da sabuwar tafiyar siyasar da ake kira The National Movement (TNM) ‘yan Najeriya suke ta tsokaci ko tambayoyi game da ita.
Yayin da wasu ke ganin za ta samar wa ‘yan Najeriya mafita a 2023, wasu cewa suke yi tana da jan aiki a gabanta.
Dokta Saidu Ahmad Dukawa masanin siyasa ne a Jami’ar Bayero ta Kano; ya yi wa Aminiya fashin-baki a kan irin fadi-tashin da tafiyar da TNM za ta iya fuskanta.
- Fina-finan Nollywood ke haddasa kisa don tsafi a Najeriya —Lai Mohammed
- An tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara
Wace irin rawa kake ganin TNM za ta taka yayin da ake tunkarar zabukan 2023?
To babbar rawar da kungiyar TNM ta su [tsohon Sanata Rabi’u Musa] Kwankwaso za ta iya takawa nan da zabukan 2023, ita ce ta kokarin samar da maja – ya zamana an sami wasu kananan jam’iyyun da dama sun hadu sun narke sun hada wata maja shigen wacce aka yi a APC.
To idan suka samu yin haka kuma ‘yan kasa suka amince musu, to za su iya girgiza jam’iyya mai mulki ta APC, kuma watakila ma su yi nasarar karbar shugabanci.
Amma wannan ya danganta da irin dan takarar da suka tsayar da karbuwarsa da kuma wadanda PDP da APC za su tsayar da tasu karbuwar.
To idan suka tsai da duk wanda ya fi wadanda APC ko PDP za su tsayar, to za su iya ba da mamaki a 2023.
Amma dai idan aka yi la’akari da [cewa] ya zuwa yanzu wadanda suka taru, wato wadanda suke da kyakkyawan tarihin siyasa a ciki ba su da yawa, wadanda suke da matsala ko kuma ba a san su ba, ko ba su taka rawar da za a gani ba duk da cewa sun taba zama gwamna a jiharsu ko sun taba zama sanata, duk wannan bai sa sun samu shuhurar da wasu daga cikinsu suka samu ba, don haka suna da aiki tukuru a gabansu.
Wadanda suka shiga wannan tafiya ta TNM sun fito daga jam’iyyu daban-daban, wace irin rawa kake ganin za su iya takawa a tafiyar?
E, da ma duk wani yunkuri yanzu da za a yi na yin sabuwar hadaka, dole zai kunshi wasu daga cikin tsofaffin ‘yan jam’iyya, ma’ana wadanda suke cikin tsofaffin jam’iyyu daban-daban
Amma abin da kawai yake akwai shi ne kyau a ce wadanda ba su rike wani mukami wato sun tafka kurakurai fiye da alherin da suka shuka ba, to ya zamana su suka fi yawa, ba kamar yanzu inda alamar ta nuna ba, cewa wadanda za a iya cewa babu laifi [a tare da su] su ne suka fi yawa ba.
Sannan kuma rawar da za su iya takawa a jam’iyyunsu daban-daban da suka fito, ai ta danganta – in dai sabuwar maja za su yi, duk sai sun fita daga jam’iyyun da suke ciki, domin ba na jin akwai wanda yake da karfin da zai janyo daya daga manyan jam’iyyun nan ta shigo wannan sabuwar tafiyar.
Saboda haka a karshe dai su ne za su fita su shiga sabuwa, wasu kuma in sun zauna, amma suka ce suna goyon bayan wannan yunkurin, to watakila za su yi anti-party ke nan, don haka da wuya a saki jiki da su a tsohuwar jam’iyyarsu kowace ce.
Don haka wannan shi ne abin da nake kyautata zaton zai faru.
Farfesa Jega ya koma jam’iyyar PRP a shekarar da ta wuce don kalubalantar APC, amma shiru ake ji zuwa yanzu.
Shigar Farfesa Attahiru Jega PRP bai hana shi shiga duk wani yunkuri da ake yi na samar da maja ba, saboda PRP a karan kanta, ita ma ba za ta iya kai bantenta ita kadai ba, don haka ire-iren su PRP ake so su fito su hadu su samar da sabuwar maja da za ta fi karfin ta APC kuma ta fi karfin PDP.
To idan aka yi wannan shi ne za a dace.
Don haka ta yiwu yana nan a PRP amma kuma yana cikin wannan yunkurin da za a samar da sabuwar maja idan sun yi nasara sai ya jagoranci ita PRP din zuwa cikin sabuwar maja, in kuma ba su yi nasara ba, watakila ya sake juyawa wani yunkurin na yin maja, ya tafi da PRP din can.
Don haka wannan babu abin damuwa a ciki kuma ai ba za a ce har yanzu shiru ba, saboda daga sanda ya shiga zuwa yau ai ba a yi wani zabe ba a kasar, ballantana a ce shiru ko bai tsaya takara ba ko ba a ga su wa suka tsayar ba.
Kafin zaben 2019 Obasanjo da wasu sun yi kokarin kirkirar irin wannan tafiya, amma tafiyar ba ta je ko ina ba, a ina aka samu matsala?
Gaskiya ne Obasanjo ya yi kokarin haka a 2019 bai yi nasara ba, kuma kafin shi Atiku ya yi kokari ya ga ya samar da wata sabuwar tafiyar da ba PDP ba APC ba, shi ma bai iya ba, ba don komai ba sai don girman Najeriya ne ya fi karfin wani mutum daya ya ce wai zai bugi kirji, ya samar da sauyi a kasar.
Ko a APC din sai da aka samu jiga-jigai guda biyu su ne da Buhari da Tinubu.
Buhari yana da goyon bayan da ba wani dan siyasa da yake da shi a arewa, Tinubu yana da goyon bayan da ba wani dan siyasa da yake da shi a kasar Yarbawa, shi ne dalilin da ya sa tafiyar ta yi nasara.
Amma ba wani yunkuri a yanzu ko wannan din da su Kwankwaso suke yi ko kuma wanda yake a karkashin kasa, wanda ake ganin alamar za a iya samun wannan.
Saboda haka ya danganta da sai kowa ya fito da nasa yunkurin, to idan aka fito, a nan ne za a samu cewa da yunkurin su wane da su wane in aka hada za a samu sakamakon da ake bukata.
Don haka muna nan muna jiran mu ga me zai faru.
Idan aka sake samun wani fitacce kamar Kwankwaso a kudu, shi ma ko ya shigo tafiyar su Kwankwaso ko kuma ya kafa wata kungiyar, amma an san yana da mutane magoya baya, kamar yadda Kwankwaso yake da su, to idan suka hadu da Kwankwaso sai su samar da abin da ake bukata.
Amma a yanzu ban ga wani a cikinsu wanda wadannan tsofaffin gwamnonin na kudu da ‘yan siyasar tasu da suka shigo tafiyar, ban ga guda daya wanda ya kai nauyin Kwankwaso ba a kudu, ma’ana nauyin da Kwankwaso yake da shi a arewa.
Wato ya fi karfin kowane daya daga cikinsu ba wanda a cikinsu yake da wannan nauyin a kudu shi ya sa ma su da kansu suka yarda, suka sa shi a gaba a matsayin shi ne jagoran tafiyar.
Saboda haka in ba wannan suka samu ba, gaskiya ban yi zaton za su kai bantensu ba su ma.
Don in aka duba za a ga kuma nauyin Kwankwaso a kasar bai kai nauyin Obasanjo ba, amma Obasanjo ya kasa, saboda haka wannan shi ne abin da mutane ya kamata su yi la’akari kuma su yi taka tsantsan ban da makauniyar biyayya da za ta kai ga batawa da ‘yan uwa da abokai, wanda kuma daga karshe za a zo a ga cewa duk ma abun ba mai yiwuwa ba ne.
Wanne irin kallo kake ganin APC da PDP za su yi wa wannan sabuwar tafiyar, kasancewar akwai ‘ya’yansu a ciki?
La budda da APC da PDP za su yi wa wannan sabuwar tafiyar kallo na cewa ga wani sabon kalubale ya taso musu, ga wasu ‘yan cikin gidansu suna so su kebe wuri guda su yo gungu su fito su yake su.
Don haka, su ma za su yi duk abin da za su yi su ga cewa sun yake su.
Saboda haka dole ne wannan tafiya ta TNM ta dauka cewa APC da PDP abokan hamayyarta ne, saboda haka ta yi shirin da za ta iya bugawa da duk su biyun kuma wannan shiri ne na zaune ba kawai inda wadansu suke ganin in sun goyi bayan mutum daya ko biyu a social media watakila ma sun yi zage-zage shi ke nan sai kowa ya bi su, ya bar APC da PDP ba.
Saboda haka aiki ne na zaune tukuru wanda in dai ana so a ‘yanto kasar sai an hadu an yi shi