APC fankon ashana ce a Bauchi – Sanga
Wani mai neman tsayawa takarar Majalisar Wakilai daga mazabar Toro a Jihar Bauchi, Injiniya Joshua Titus Sanga ya bayyana Jam’iyyar APC a matsayin fankon ashana da ba za ta kai bantenta ba a zaben 2019 a jihar. Injiniya Sanga ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci ofishin Aminiya da ke Jos a ranar Litinin […]

Wani mai neman tsayawa takarar Majalisar Wakilai daga mazabar Toro a Jihar Bauchi, Injiniya Joshua Titus Sanga ya bayyana Jam’iyyar APC a matsayin fankon ashana da ba za ta kai bantenta ba a zaben 2019 a jihar.
Injiniya Sanga ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci ofishin Aminiya da ke Jos a ranar Litinin da ta gabata. Ya ce, “APC a Jihar Bauchi ba ta tsinana komai ba, babu ruwan sha, babu hanyoyi, babu asibitoci, babun ma ta yi yawa. Don haka jam’iyya ce kamar fankon ashana, ba ta da amfani. Ba za a sha wata wahala wajen kayar da ita a zabe ba.”
Sanga ya ce ya yanke shawarar fitowa neman takarar Majalisar Wakilai ce domin ya kawo wa mazabarsa manyan ayyuka daga Gwamnatin Tarayya da mazabar ta gaza amfana da su tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999.
Injiiya Sanga wanda ya yi digiri na biyu kan Gine-Gine a Jami’ar Cibil Engineering Management Unibersity da ke birnin Wolberhamton a kasar Ingila, ya ce, idan aka zabe shi zai mayar da hankali wajen tabbatar da shugabanci nagari da bin doka da oda da tabbatar adalci ga ’yan kasa da kuma tabbatar da an samu hadin kan ’yan kasa.
Ya ce, “Ba za a samu nagartacciyar dimokuradiyya ba, matukar babu bangaren dokok, don haka idan aka zabe ni zan bayar da gudunmawata wajen ganin a samar da ayyukan raya kasa da masana’antu don ganin matasa sun samu aikin yi.”