APC na kan gaba a kananan hukumomi 6 a Katsina
INEC ta fara fitar da sakamakon zaben kujerar shugaban kasa na Jihar Katsina
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar da sakamakon zaben kujerar shugaban kasa a wasu daga cikin kananan hukumomi 34 da ke Jihar Katsina.
Sakamakon kananan hukumomin da suka hada da Sandamu, Ɗandume, Mashi, Dsnmusa, Rimi da kuma Kurfi, ya nuna zuwa yanzu jam’iyar APC ce ke kan gaba.
- Kwankwaso ya cinye karamar hukumar Ganduje
- INEC ta ayyana zaben Majalisar Wakilai ‘inconclusive’ a Kogi
APC wadda Bola Ahmad Tinubu ke wa takara ta samu kuri’u 80,832, inda ya ba wa abokin takararsa na jam’iyar adawa ta PDP Atiku Abubakar tazara da kuri’a 20,920.
Atiku wanda ya zo na biyu na da kuri’u 59,912 dai Rabiu Kwankwaso na NNPP ya zo na uku da kuri’u 8191.
Ya zuwa yanzu dai cibiyar tattara sakamakon zabe ta INEC ta dakatar da aikin, inda ta tafi sai zuwa anjima za ta ci gaba.