APC na shirin yin magudin zabe a Katsina- shugaban PDP na jihar
Jam’iyyar adawa ta PDP reshen jihar Katsina ta ce, zaben da aka yi wa shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar wani shiri ne sama wa Shugaba Buhari kuri’u da Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari, da akwai alamu yin shirin magudi a zaben 2019, sakamakon furucin da Oshiomhole ya yi na cewa, Buhari […]
Jam’iyyar adawa ta PDP reshen jihar Katsina ta ce, zaben da aka yi wa shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar wani shiri ne sama wa Shugaba Buhari kuri’u da Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari, da akwai alamu yin shirin magudi a zaben 2019, sakamakon furucin da Oshiomhole ya yi na cewa, Buhari zai samu kuri’u kaso 100 daga jihar.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Salisu Magijiri, ya bayyana wa majiyarmu cewa, duk fargabar da suke yi ya tabbata akan shirin yin magudi sakamakon jawabin da Oshiomhole ya yi kwanan nan.