APC, NNPP sun umarci magoya bayansu a Kano su tsare ƙuri’unsu
Jam’iyyun APC da NNPP a jihar Kano sun umarci magoya bayansu da su ɗunguma cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe domin kaucewa maguɗi. Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya bada umarnin a madadin APC yayinda jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana a madadin NNPP. A sanarwar da ya fitar, […]
Jam’iyyun APC da NNPP a jihar Kano sun umarci magoya bayansu da su ɗunguma cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe domin kaucewa maguɗi.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya bada umarnin a madadin APC yayinda jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana a madadin NNPP.
A sanarwar da ya fitar, Muhammadu Garba ya ce kiran ya zama wajibi saboda kare ƙuri’un da suka kaɗa.
Shi ma Kwankwaso ya saki wani gajeren bidiyo ne inda ya ce sakamakon akwatunan da aka bayyana ya ba NNPP ƙwarin gwiwar samun nasara a zaɓen.
Don haka ya umarce magoya baya su bai wa ƙuri’unsu kariya a matakan mazaɓu, ƙananan hukumomi, da kuma jiha.
Aminiya ta ruwaito cewa an kammala zaɓen a mafi yawan rumfunan zaɓen dake faɗin jihar Kano, in da kuma aka shiga tattara sakamako.
Kuma kodayake akwai jam’iyyu da yawa dake takarar kujerar gwamnan jihar Kano, ƴar manuniya ta nuna cewa tsakanin Nasiru Yusuf Gawuna na APC da Abba Kabir Yusuf na NNPP ake sa ran samun wanda zai yi nasara.