APC ta bayar da ratar fiye da kuri’u dubu 200 a Zaɓen Gwamnan Kogi
Sakamakon zaben kananan hukumomi uku kacal ne suka rage a yayin da INEC ta dage zaman tattara sakamakon.
Jam’iyyar APC ce ke kan gaba da gagarumin rinjaye a sakamakon zaɓen kananan hukumomi 18 na Jihar Kogi wanda Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana kawo yanzu.
Usman Ododo, dan takarar jam’iyyar mai mulki, ya samu nasara a kananan hukumomi 11, sai Muri Ajaka na jam’iyyar SDP da ya samu nasara a kananan hukumomi shida, yayin da kuma Leke Abejide na jam’iyyar ADC ya samu a karamar hukumar daya.
- Zaɓen Gwamna: An yi garkuwa da wasu jami’an INEC a Bayelsa
- Hope Uzodinma Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Imo
Ya zuwa yanzu dai, Ododo ya samu kuri’u 409,450, Ajaka kuwa ya samu 208,503 yayin da Dino Melaye na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 41,925 kacal.
INEC ta dage zaman tattara ragowar sakamakon zaben na kananan hukumomin Kogi uku da suka yi saura.
Ga dai sakamakon zaben kananan hukumomin da INEC ta fitar kawo yanzu:
Okehi
APC 53,0623
PDP: 2,722
SDP: 153
Yagba East
APC: 7,096
PDP: 2,615
SDP: 312
Ijumu
APC 10,524
PDP: 6,909
SDP: 356
Mopa-Muro
APC: 5,077
PDP: 1,562
SDP: 253
Adavi
APC: 101,156
PDP: 1,005
SDP: 268
Ofu
APC: 5,245
PDP: 293
SDP: 28,768
Koton Karfe
APC: 14,769
PDP: 2,974
SDP: 8,441
Bassa
APC: 9,519
PDP: 3,605
SDP: 7,543
OmalaSakamamkon zabe
APC: 2,902
PDP: 832
SDP: 18,160
Olamaboro
APC: 5,572
PDP: 1,376
SDP: 22,173
Ankpa
APC: 8,707
PDP: 3,654
SDP: 43,258
Okene
APC: 138,416
PDP: 1,463
SDP: 271
Dekina
APC: 9,174
PDP: 499
SDP: 47,480
Ajaokuta
APC: 23,211
PDP: 483
SDP: 8,869