APC ta bukaci Buhari ya kafa dokar ta baci a Akwa Ibom
Sakamakon rikicin da ya addabi majalisar dokokin jihar Akwa Ibom a ranar Talata, jam’iyya mai mulki ta APC ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya kafa dokar ta baci a jihar. Shugaban jam’iyyar APC na jihar Ini Okopido ne ya sanar da hakan ganin cewa, Gwamnan jihar Udom Emmanuel ya gaza magance rikicin ‘yan […]
Sakamakon rikicin da ya addabi majalisar dokokin jihar Akwa Ibom a ranar Talata, jam’iyya mai mulki ta APC ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya kafa dokar ta baci a jihar.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Ini Okopido ne ya sanar da hakan ganin cewa, Gwamnan jihar Udom Emmanuel ya gaza magance rikicin ‘yan majalisar dokokin jihar.
Ini Okopido, ya ce, lokacin da Gwamnan jihar ya ziyarci majalisar jihar ya shiga ne tare da ‘yan daba da jami’an ‘yan sanda da jami’an tsaron DSS da wasu Kwamnishinoni, wanda hakan ya janyo rikici tsakanin ‘yan jam’iyyar APC da suka fice daga PDP daga majalisar.