APC ta dasa mana ’yan takarar Shugaban kasa a PDP – Gwamnan Ribas

A ranar Talatar da ta gabata ce Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya nanata cewa fadar Shugaban kasa da Jam’iyyar APC sun dasa ’yan takarar Shugaban kasa a a jam’iyyarsu ta PDP. Ya ce amma dukan shugabannin jam’iyyar a jihar za su tantance dan takaran Shugaban kasa da za su zaba a zaben fid-da-gwanin jam’iyyar […]

APC ta dasa mana ’yan takarar Shugaban kasa a PDP – Gwamnan Ribas
APC ta dasa mana ’yan takarar Shugaban kasa a PDP – Gwamnan Ribas

A ranar Talatar da ta gabata ce Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya nanata cewa fadar Shugaban kasa da Jam’iyyar APC sun dasa ’yan takarar Shugaban kasa a a jam’iyyarsu ta PDP. Ya ce amma dukan shugabannin jam’iyyar a jihar za su tantance dan takaran Shugaban kasa da za su zaba a zaben fid-da-gwanin jam’iyyar da ke tafe.

Gwamnan a zantawa da manema labarai a Fatakwal, ya nanata cewa ba zai taba yarda a yaudare shi ko a wautar da shi ba, yana mai cewa yana sane da duk abin da fadar Shugaban kasa da APC ke shiryawa wajen tabbatar da cewa wani dan APC ya samu nasarar a zaben fid-da-gwani na PDP. 

Wike ya ce, “Amma abu daya da nake son ku rike shi ne cewa ba zan taba yarda a wautar da ni ba, ba zan taba yarda a yaudare ni ba; Ina da cikakkiyar masaniya a kan abin da yake faruwa. Ina kuma sane da yunkurin da APC ke yi na dasa mana danta don ya tsaya takara a PDP. Ba zan ambaci yadda wani babban jami’in tsaro na kasar nan wanda yake gaya min wanda ya kamata in goya wa baya a PDP ba. Wannan ba abin mamaki ba ne a matsayina na Gwamna sannan wani jami’in tsaro ya gaya min wanda ya kamata in goya wa baya? Babban jami’in da APC ke sarrafa shi, sannan zai zo ya gaya mini wanda zan goya wa baya? Wannan abin mamaki ne.”

Gwamna Wike ya kara da cewa akwai wadansu ’yan takarar da Shugaba Buhari yake daukar nauyinsu a PDP. Yana mai cewa babu wanda za su bari ya yaudari ko mutum daya daga al’ummar Jihar Ribas wajen nuna musu wanda za su goya wa baya a zaben fid-da-gwani na PDP da ke tafe. 

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa