APC ta gargadi ’yan takara masu hada hotunansu da na Buhari

Jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta gargadi masu takara da suka fito daga wasu jam’iyyu su daina hada hotunansu da na dan takararta na Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari. Shugaban jam’iyyar, Dokta Mustafa Inuwa ne ya yi wannan gargadi a waurin taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta yi a otel na Liyafa a […]

APC ta gargadi ’yan takara masu hada hotunansu da na Buhari
APC ta gargadi ’yan takara masu hada hotunansu da na Buhari

Jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta gargadi masu takara da suka fito daga wasu jam’iyyu su daina hada hotunansu da na dan takararta na Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari. Shugaban jam’iyyar, Dokta Mustafa Inuwa ne ya yi wannan gargadi a waurin taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta yi a otel na Liyafa a ranar Litinin inda ya ja hankalin ’yan takarar wasu jam’iyyu da ke lika hotunansu da na Buhari su daina yin haka nan take ko su fuskanci matakin shari’a. 

Dokta Mustafa Inuwa ya ce, in har suna so suna iya shigowa jam’iyyar, amma ba su rika ungulu da kan zabo ba. “Mu Jam’iyyar APC muke yi sak, babu ungulu da kan zabo, muna kiran magoya bayan APC a duk inda suke su zabi ’yan takarar da jam’iyyar ta tsayar tun daga kasa har sama,” inji shi.
Shugaban ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar su yi watsi da kira ko shirin da wasu ’yan takarar da suka fito daga wasu jam’iyyu ke yi cewa su zabi Buhari a sama amma saura su zabi nasu ’yan takarar. “Ina so jama’a su sani cewa in Buhari ya zama Shugaban kasa amma bai da mataimakan da suke tare da shi babu abin da zai iya yi, hasali ma suna iya tsige shi su kawo nasu su sanya. Magoya bayan nan ba ma kamar ’yan Majalisar Tarayya da Sanatoci da Gwamnoni da sauransu. Don haka jama’a su gane wannan makirci.
dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam’iyyar APC, Alhaji Aminu Bello Masari ya yi kira ga abokan takara da ba su samu nasara ba da su dauka haka Allah Ya hukunta kuma su zo su hada hannu su yi aiki tare domin ganin jam’iyyar ta yi nasara a duk zabubbukan da za a yi a watan gobe.
Aminu Masari wanda ya ce, tuni ya fara ziyartar gidajen abokan takararsa don samun hadin kai a tsakaninsu don yi wa jam’iyya da al’ummar kasar nan aiki.
Ya gabatar da mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu, inda ya yi fatan za su samu goyon baya da hadin kan al’ummar Jihar Katsina don su kafa gwamnati tare da kawo canji mai ma’ana a jihar.
A jawabin daya daga cikin wadanda suka yi takara a zaben fidda gwani, Kuma tsohon Maitaimakin Gwamnan Jihar Ambasada Abdullahi Garba Aminchi ya ce, shi da magoya baya da wasu abokan da suka yi takarar tare suna goyon Alhaji Aminu Masari da Jam’iyyar APC don ganin sun samu nasarar kafa gwamnati daga kasa har sama.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista