APC ta gaza- Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasa, Gudloock Jonathan ya ce mulkin APC, a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza wajen cika alkawuran da ta dauka wa ‘yan Najeriya. Tsohon shugaban ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake karbar bakuntan tsohon Minsitan Ilimi, Farfesa Tunde Adeniran, wanda ke neman zama shugaban Jam’iyyar PDP a taronta na […]

APC ta gaza- Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasa, Gudloock Jonathan ya ce mulkin APC, a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza wajen cika alkawuran da ta dauka wa ‘yan Najeriya.

Tsohon shugaban ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake karbar bakuntan tsohon Minsitan Ilimi, Farfesa Tunde Adeniran, wanda ke neman zama shugaban Jam’iyyar PDP a taronta na kasa da ke tafe.

A cewar Jonathan, maimakon APC ta inganta rayuwar al’ummar Najeriya, sai ta kara jefa su cikin wahala da talauci da matsin tattalin arziki.

Jonathan ya kara da cewa wadanda suke ta cece-kuce a kan cewa ya gaza a lokacin da yake mulki, su ne yanzu duk suka rude su ka rasa yadda za su yi.

“Yanzu ana sayan litan mai Naira 145. Babu wani ci gaba a bangaren wutar lantarki.

“Ya kamata mu samu shugabannin jam’iyya na kwarai. Jam’iyyar PDP ta kokarta lokacin tana mulki tsakanin 1999 zuwa 2015. Wadanda kuma suke cewa ba mu iya ba, su yanzu me suka yi?