APC ta gudanar da zaben ‘yan takarar kananan hukumomi a Filato

A shirye-shiryen da ake yi, na gudanar da zaben shugabannin  kananan hukumomin Jihar Filato 17, wanda za ayi a ranar 17 ga watan 2 na sabuwar shekara mai zuwa. Jam’iyyar APC reshen jihar ta gudanar da zaben wadanda zasu tsaya mata a wannan zabe, a ranar Asabar da ta gabata. Wakilinmu ya ganewa idonsa yadda […]

APC ta gudanar da zaben ‘yan takarar kananan hukumomi a Filato

A shirye-shiryen da ake yi, na gudanar da zaben shugabannin  kananan hukumomin Jihar Filato 17, wanda za ayi a ranar 17 ga watan 2 na sabuwar shekara mai zuwa. Jam’iyyar APC reshen jihar ta gudanar da zaben wadanda zasu tsaya mata a wannan zabe, a ranar Asabar da ta gabata.

Wakilinmu ya ganewa idonsa yadda wakilan jam’iyyar masu zabe suka jefa kuru’unsu a cikin tsari ba tare da samun wata hatsaniya ba, har aka kammala zaben. A wuraren da aka gudanar da zaben a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa.

To amma wakilin namu ya ga yadda aka tsaurara makatan tsaro a wajen da aka gudanar da zabukan a karamar hukumar Jos ta Arewa. 

Tuni aka sami sakamakon zaben a kananan hukumomi 15 da aka gudanar da zaben. A karamar hukumar Jos ta Arewa an zabi Alhaji Shehu Bala. A yayin da aka zabi Mista Chindo Gona a karamar hukumar Bassa.

Sauran wadanda aka zaba din sun hada da Mista Choji Dachung a karamar hukumar Jos ta Kudu, Miskoom Aled a karamar hukumar Shendam, Ado Abubakar a karamar hukumar Wase, Amos Kparmim a karamar hukuma Langtang ta Arewa, Ibrahim Agwom a karamar hukumar Jos ta Gabas, Isaac Kwallu karamar hukumar kuan Pan, Ezekiel Mandyau a karamar hukumar Barikin Ladi, Lawrence Danat a karamar hukumar Mangu.

Har’ila yau an zabi John D. Damap a karamar hukumar Panshin, Emmanuel Wambutda a karamar hukumar Kanke, Yusuf Manchen a karamar hukumar Bokkos, Gwallson Mafeng a karamar hukumar Riyom da Ezekiel bongap a karamar hukumar Mikang.

Da yake zantawa da manemna labarai, sakataren jam’iyyar ta APC a Jihar Filato, Alhaji Bashir Musan Sati ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda aka gudanar da zaben lafiya. Ya ce a kananan hukumomin Kanam da Langtang ta Kudu da ba a sami gudanar da zaben ba, nan gaba za a bayyana ranar da za gudanar da zaben.

A zantawarsa da wakilinmu kan wannan zabe, tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta arewa da Bassa Honarabul Lumumbar Dah Adeh ya bayyana cewa tun da aka dawo  mulkin dimokuradiyya a Jihar Filato, ba a taba zaben ‘yan takarar jam’iyya kamar irin wannan ba, wajen yin adalci.

Ya ce an tsara wannan zabe yadda ya kamata, ta yadda ba za a sami wata matsala ba. “Wannan zabe ya bambanta da sauran zabubbukan tsayar da ‘yan takarar da aka yi a baya. Babu shakka yadda aka gudanar da wannan zabe zai baiwa jam’iyyar APC damar lashe wannan zabe a dukkan kananan hukumomin jihar nan’’.

Shi ma a zantawarsa da wakilinmu kan wannan zabe, wani jigon APC kuma Garkuwan Al’ummar Hausa Fulani na yankin Pengana dake karamar hukumar Bassa, Alhaji Ya’u Bala PJ Jingir ya bayyana cewa an yi zabe mai tsafta a wannan zabe da aka gudanar. Ya ce a wannan zabe an baiwa talakawa dama sun zabi ‘yan takarar da suke so, ba tare da tursasawa kowa ba.

Ya ce da ma gwamnan Filato Simon Lalong ya ce kowa ya je ya nemi jama’a, shi ba shi da wani dan takara. “Babu shakka yadda wannan zabe ya gudana ya nuna cewa gwamna ya cika maganarsa ta baiwa kowa ‘yancinsa a wannan zabe.