APC ta hana magoya bayan Gwamna Fubara takarar Majalisar Dokokin Jihar a Ribas 

Sai dai ’yan takara 33, mafi yawansu magoya bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kuma yawancinsu mambobin majalisar masu ci ne, an amince da su shiga zaben fid-da-gwani.

APC ta hana magoya bayan Gwamna Fubara takarar Majalisar Dokokin Jihar a Ribas 

Kwamitin tantance ’yan takara na Jam’iyyar APC ya hana mutum 65 magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara shiga neman takarar Majalisar Dokoki na Jihar Ribas.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan waɗanda aka hana shiga takarar magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara ne, ciki har da tsohon Shugaban Majalisar Dokoki na Jihar na tsagin da ya balle, Victor Oko Jumbo, da kuma tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Obio/Akpor, Chijioke Kemzunum Ihunwo.

Rahoton kwamitin tantancewar, wanda Rt. Hon. Muraina Ajibola da wasu mambobi uku suka sanya hannu, ya bayyana cewa an hana su shiga takarar ne saboda rashin cika sharuɗɗan, ciki har da matsalar sahihancin takardar rantsuwar kotu, rashin daidaiton ranar haihuwa, da kuma matsalolin takardun tsayawa takara.

Sai dai ’yan takara 33, mafi yawansu magoya bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kuma yawancinsu mambobin majalisar masu ci ne, an amince da su shiga zaben fid-da-gwani.

Kwamitin Ajibola ya ce an tantance takardun su kuma sun cika sharuddan jam’iyya.

Jimillar ’yan takara 98 ne suka sayi fom don shiga zaben fid-da-gwani na APC a Majalisar Dokokin Ribas, inda aka tantance su a sakatariyar jam’iyyar da ke Fatakwal a ƙarshen mako.

Wannan mataki ya ƙara tayar da jijiyoyin wuya a siyasar jihar Ribas, kafin zaɓen 2027, inda aka ga magoya bayan Wike sun samu nasara a tantancewar, yayin da na Fubara aka kawar da su.

Wani jigo na APC a Ribas da ke goyon bayan Gwamna Fubara ya shaida wa wakilinmu cikin sirri cewa abin da jam’iyyar ke yi yanzu na iya sauƙaƙa wa kowace jam’iyyar adawa samun nasara a jihar a zaɓen 2027.

Ya ce: “Ba za ka kori manyan masu kawo jama’a cikin jam’iyya ba saboda kana son faranta wa wani ɓangare rai, sannan ka yi tsammanin za su zauna su yi aiki don nasarar waɗanda suka danne su.

“Idan ba a kula ba, APC ta daɓa wa kanta wuƙa, kuma sakamakon zai bayyana a zaben gaba.”

Waɗanda aka amince da su sun haɗa da: Maol Dumle, Major M. Jack, Nwabochi Frankline, Ofiks K. Christopher, Enemi Alabo George, Tonye Smart Adoki, Tekenari W. Granville, Azeru Opara, Igwe Obey Aforji, Opuende Lolo Isaiah, Ukalikpe Napoleon, Hope Ugwumadu, Kenneth Minimah, Justina Aniton Okorji, Onyema Rex Nwankwo, Jumbo Soparagha, Wami Solomon, Gift Esede Ali, Ejekwu Chisa Nathan da Peter E. Abbey.

Sauran sun haɗa da: Loolo Bulabari Henrietta, Barida Alice Samuel, Ohanuna Bright, Kue Yeghene, Nwankwo Chimezie C., Emeji Gloria Chika, Ejekwu, Ezebunwo Leslie, Okpokipou Peters, Arnold O. Davids, Gerald C. Oforji, Amadi Promise Amadi, Opuene Thompson Atekebo da Amakri Awowari.