APC ta kaddamar da yakin zaben Buhari da Bagudu a Kebbi

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi ta kaddamar da yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu karo na biyu a zaben bana a Karamar Hukumar Argungu, inda daruruwan mutanen suka halarta. Taron kaddamar da yakin neman zaben ya kara armashi ne bayan tsohon Ma’ajin Jam’iyyar PDP na Kasa kuma tsohon dan […]

APC ta kaddamar da yakin zaben Buhari da Bagudu a Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi ta kaddamar da yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu karo na biyu a zaben bana a Karamar Hukumar Argungu, inda daruruwan mutanen suka halarta.

Taron kaddamar da yakin neman zaben ya kara armashi ne bayan tsohon Ma’ajin Jam’iyyar PDP na Kasa kuma tsohon dan takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP kuma tsohon Minista Alhaji Buhari Bala ya canja sheka zuwa Jam’iyyar APC.                                                                                                                         Yayin kaddamar da yakin neman zaben an kuma kaddamar da ayyukan hanyoyin mota da gwamnatin Gwamna Atiku Bagudu ta gudanar a Masarautar Argungu.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, Alhaji Bala Sani Kangiwa ya roki mutanen da suka halarci taron da na Masarautar Argungu su zabi Gwamna Atiku Bagudu da kuma Shugaba Muhammadu Buhari a zaben bana.

A jawabin, Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamna Bagudu Alhaji Suleiman Muhammad Argungu ya bayyana cewa, “A karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Atiku Bagudu Jihar Kebbi ta samu ci gaba musamman a bashin da ake ba manoma na noman rani da damana da ake kira (Anchor Borrowers) wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito da shi, kuma Gwamnatin Jihar Kebbi da Babban Bakin Najeriya suka yi hadin gwiwa domin tabbatar da cewa shirin ya yi tasiri a jihar.”

Gwamna Atiku Bagudu ya jagorancin mambobbin Jam’iyyar APC domin kai wa Mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ziyara domin ya sanya musu albarka.

Kuma Gwamna Bagudu ya raba wa hakimai 72 da ke Masarautar Argungu Naira dubu 200 kowanensu domin sayen babur, inda kudadensu suka kai Naira milyan 67 kuma ya raba wa hakiman masarautar Argungu da ke Jihar Kebbi.

Daga karshe Gwamnan ya gode wa mutanen jihar bisa goyon baya da suke ba gwamnatin APC.