Zagon Kasa: APC ta kori Sanata Danjuma Goje
Jam’iyyar APC reshen Gundumar Kashere, mazabar Sanata Danjuma Goje, ta kore shi daga jam’iyyar.
Jam’iyyar APC ta kori Sanata Danjuma Goje a matakin Gundumar Kashere da ke Jihar Gombe kan zargin zagon kasa ga jam’iyyar.
Shugaban Jam’iyyar APC na gundumar Kashere, Tanimu Abdullahi, ya ce an kori Sanata Goje, wanda tsohon gwamnan jihar ne, bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa a lokacin zaben khugaban kasa da na gwamna.
Tanimu Abdullahi ya sanar da hakan ne a ranar Talata a gundumar ta Kashere, inda ya ce suna zargin Goje da yiwa APC zagon kasa tun kafin zabe har lokacin zabe.
Ya ce ko a lokacin da zababben Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya kai ziyarar yakin neman a Gombe Gojen bai zo ba, haka kuma ya ki zuwa duk tarurruka da jam’iyyar ta yi ba.
Tanimu, ya ce sun yi wa tsohon gwamnan jan kunne a kan abun da yake yi amma bai dai na ba, sun kuma gayyace shi gaban kwamiti na mutum biyar da aka kafa don ya kare kan sa, amma bai mutunta su ya saurare su ba.
“Yaransa ma a lokacin zaben cewa suke yi Goje kawai maimakon su ce ayi APC Sak, daga sama har kasa, wanda hakan ya sa duk ’yan takarar jam’iyyar APC a mazabar Sanatan ta Kanon Kashere banda shi kansa Goje babu wani wanda ya ci zabe” in ji shi.
Tanimu Abdullahi, ya kara da cewa hatta Usman Bello Kumo dan takarar majalisar Tarayya bai ci zabe ba, Tinubu bai ci zabe ba a jihar, wanda hakan ya kara tabbatar da zagon kasar da Goje ya yi.
Shugaban jam’iyya na gundumar ya ce da amincewar daukacin shugabanin jam’iyyar na gundumar ta kashere ne suka korGoje bisa dogaro da kundin tsarin mulkin jam’iyyar sashi na 21 karamin kashi na 1 da na 2. dana 3.