APC ta kuduri aniyar kawo canji a Jihar Katsina

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Dokta Mustafa Muhammad Inuwa ya ce jam’iyyar tana nan daram kuma za ta kawo canjin gwamnati a jihar, ba kamar yadda wasu ke tsammani ba. Dokta Mustafa Inuwa ya shaida wa manema labarai haka ne bayan kammala taron farko na shugabannin jam’iyyar bayan da aka zabe su a ranar […]

APC ta kuduri aniyar kawo canji a Jihar Katsina
APC ta kuduri aniyar kawo canji a Jihar Katsina

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Dokta Mustafa Muhammad Inuwa ya ce jam’iyyar tana nan daram kuma za ta kawo canjin gwamnati a jihar, ba kamar yadda wasu ke tsammani ba. Dokta Mustafa Inuwa ya shaida wa manema labarai haka ne bayan kammala taron farko na shugabannin jam’iyyar bayan da aka zabe su a ranar Talatar makon jiya.
Shugaban ya ce, Jam’iyyar APC ta dinke wuri guda, sabanin yadda wasu ke fata ta mutu, in aka yi zaben shugabanninta. “Muna nan a matsayinmu na tsintsiya mai madauri daya. Babu bangare-bangaren da ake tunanin zai raba mu,” inji shi.
Dokta Mustafa ya ce, duk da babu wanda ya yi kuka a kan zaben, jam’iyyar na shirye-shiryen fuskantar kalubalen zaben kananan hukumomin jihar da za a yi nan gaba kadan, inda ya yi fatan jam’iyyar ta kawo canji a jihar.
Dokta Mustafa ya ce, mutanen jihar na fuskantar halin rashin tsaro da rashin ilimi da sauransu. “Akwai ma’aikacin wata karamar hukuma da ya ce, kusan su 300 suka yi ritaya, amma babu wanda aka biya, amma gwamnati na cewa ba a bin ta ko kwabo,” inji shi.
Ya ce, sun kafa kwamitocin da za su ba da shawara a kan yadda jam’iyyar za ta ci gaba da gudanar da harkokinta don kawo canji a fuskoki daban-daban ba wai na gwamnati kadai ba. “Za mu tabbatar cewa jam’iyya na karfi kuma ta kawo canji, domin ba a iya kafa gwamnati ba tare da jam’iyya ba, kamar yadda ba za a samu kyakkyawar jam’iyya ba tare da kyakkyawan jagoranci ba,” inji shi.
Ya yi kira a samu hadin kai a tsakanin jam’iyyun siyasa da hukumar zabe da jami’an tsaro da kafofin watsa labarai da sauran masu ruwa da tsaki a jihar, musamman a lokacin zabe.
Dokta Mustafa Inuwa ya ce, “APC za ta yi siyasar jama’a ce ba ta kwamfuta ba, inda za mu bi jama’a har inda suke domin neman goyon bayansu don kawo canji a Jihar Katsina”.