APC ta lashe duk kujerun kananan hukumomi a zaben Sakkwato
APC ta lashe duk kujerun ciyamoni da kansiloli a zaben kananan hukumomin Jihar Sakkwato.

APC
Jam’iar APC ta lashe duk kujerun zaben shugabannin kananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Sakkwato.
Shugaban Hukumar Zaben Jihar Sakkwato, Aliyu Suleiman, ya sanar a ranar Litinin cewa APC ta yi nasara a daukacin kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar, kamar yadda hukumar zaben jihar.
A cewarsa, ’yan takarar APC ne suka lashe zaben kananan hukumomi 23 da kujerun kansiloli da ke fadin jihar, a zaben da jam’iyyu 15 suka fafata.
Bayan sanar da sakamakon zaben hukumar ta mika wa zababben jagororin kananan hukumomin takardar shaidar cin zabe.
- Tinubu ya fara shirin sauke wasu ministocinsa
- Kotu ta kori buƙatar tsige Ganduje daga shugabancin APC
- Sojoji sun kama ’Yan Yahoo 150 a kusa da bariki a Delta
Da La’asar din Litinin din nan ake sa ran rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomin.