APC ta lashe zaben cike-gurbi na Majalisar Kebbi

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) a Jihar Kebbi ta bayyana Alhaji Samaila Salihu Bui na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na dan Majalisar Dokokin Jihar daga karamar Hukumar Arewa.Jam’iyyar APC ta lashe zaben ne da kuri’a dubu 20 da 577, yayin da dan takarar Jam’iyyar PDP Sulaiman Mohammed Yeldu ya […]

APC ta lashe zaben cike-gurbi na Majalisar Kebbi
APC ta lashe zaben cike-gurbi na Majalisar Kebbi

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) a Jihar Kebbi ta bayyana Alhaji Samaila Salihu Bui na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na dan Majalisar Dokokin Jihar daga karamar Hukumar Arewa.
Jam’iyyar APC ta lashe zaben ne da kuri’a dubu 20 da 577, yayin da dan takarar Jam’iyyar PDP Sulaiman Mohammed Yeldu ya samu kuri’a dubu 10, da 362, kamar yadda babban jami’in zaben Usman Umar Kardi ya bayyana wa manema labarai a ofishin hukumar da ke karamar Hukumar Arewa da ke garin Kangiwa Kebbi.
A ranar Asabar da ta gabata ne aka gudanar da zaben cike gurbin sakamakon rasuwar dan majalisar yankin marigayi Abdullahi T. Yeldu na Jam’iyyar APC a watan Maris na bara.
An yi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a, sai dai Hukumar Zaben ta yi wani sabon shiri, maimakon da sai an fara tantance masu kada kuri’a daga baya a zo a kada kuri’a, a wannan lokaci da zarar an tantance mutum sai ya je ya kada kuri’arsa ya wuce.