APC ta lashe zaben duk kananan hukumomin Ekiti

Jam’iyyar APC ta lashe daukacin kujerun shugabannin kananan hukumomi da na kansiloli a zaben da aka gudanar a Jihar Ekiti

APC ta lashe zaben duk kananan hukumomin Ekiti

Jam’iyar APC a ta yi nasarar lashe zaben dukkan kujerun shugabannin kananan hukumom 16 da yankunan raya karkara 22 da ke Jihar Ekiti.

Jami’iyyar ta kuma lashe kujerun Kansiloli 177 da ke jihar a zaben da a aka gudanar a jihar.

Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Ekiti (EKSIEC), Alkali Cornelius Akintayo (mai ritaya) shi ne ya bayyana haka a hedikwatar hukumar zaben jihar (EKSIEC) da ke garin Ado-Ekiti babban birnin jihar.

Da yake karbar sakamakon zaben daga hannun jami’an da suka gudanar da zaben a kananan hukumomin, Alkali Cornelius Akintayo mai ritaya ya ce Jam’iyun siyasa 11 ne suka fafata a zaben da suka hada da LP da ZLP da AA da ADC da NNPP da sauransu.

Shugaban Hukumar zaben ya jinjina wa irin rawar da jami’an tsaro da su kansu jam’iyun siyasa da ’yan jarida da dukkan masu ruwa da tsaki suka taka wajen tabbatar da ganin an gudanar da zaben lami lafiya.

Ya ce nan ba da dadewa ba Hukumar za ta bayyana ranar da’ yan takarar da suka yi nasara za su karbi takardun shaidar lashe zaben.

Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu