APC ta lashe zaben Gwamnan Bayelsa – INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa INEC ta sanar da Dan takarar Gwamnan jihar Bayelsa na jam’iyyar APC, David Lyon, ne a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar. David Lyon ya samu kuri’u 352,552 da suka ba shi damar doke sauran yan takara da suka hada da Mista Duoye Diri na jam’iyyar PDP […]

APC ta lashe zaben Gwamnan Bayelsa – INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa INEC ta sanar da Dan takarar Gwamnan jihar Bayelsa na jam’iyyar APC, David Lyon, ne a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar.

David Lyon ya samu kuri’u 352,552 da suka ba shi damar doke sauran yan takara da suka hada da Mista Duoye Diri na jam’iyyar PDP wanda ya zo na biyu da kuri’u 143,172.

Kafin David Lyon, ya sauya jam’iyya ya kwashe shekara 20 a cikin jam’iyyar PDP a jihar.

David Lyon, ya lashe kananan Hukumomin da suka hada da: Nembe, Brass, Southern Ijaw, Yenagoa, Ekeremor da Ogbia. Yayin da abokin takararsa na PDP ya lashe Kananan Hukumomin Sagbama da Kolokuma/Opokuma.