APC ta lashe zaben Gwamnan Kogi – INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa INEC ta sanar da Dan takarar Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar. Baturen zaben jihar Kogi kuma shugaban jami’ar Ahmadu Bello Zariya Farfesa Ibrahim Garba, ne ya sanar da sakamakon kamar haka. Dan takarar Gwamnan APC Yahaya Bello, […]
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa INEC ta sanar da Dan takarar Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar.
Baturen zaben jihar Kogi kuma shugaban jami’ar Ahmadu Bello Zariya Farfesa Ibrahim Garba, ne ya sanar da sakamakon kamar haka. Dan takarar Gwamnan APC Yahaya Bello, ya lashe zaben da kuri’u 406, 222. Yayin da abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Injiniya Musa Wada, ya samu kuri’u 189,704.