APC ta lashe zabukan cike gurbi a Katsina, Bauchi da Kwara
Jam’iyya mai mulki ta APC ta lashe zabukajn cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar da gaba ta a jihohin Katsina da Bauchi da Kwara. A jihar Bauchi Yusuf Nuhu dan takarar jam’iyyar APC daga mazabar Toro ne ya lashe zaben da kuri’u 22,317. A jihar Katsina State, Abubakar Yahaya Kusada daga APC ya samu […]
APC
Jam’iyya mai mulki ta APC ta lashe zabukajn cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar da gaba ta a jihohin Katsina da Bauchi da Kwara.
A jihar Bauchi Yusuf Nuhu dan takarar jam’iyyar APC daga mazabar Toro ne ya lashe zaben da kuri’u 22,317.
A jihar Katsina State, Abubakar Yahaya Kusada daga APC ya samu kuri’ 48,518 inda ya zama wanda ya lashe zaben a mazabun Kusada da Kankiya da Ingawa.
A Kwara dan takarar APC, Mista Raheem Olawuyi Ajuloopin, ne lashe zaben a mazabun Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-Ero da kuri’u 21,236.