APC ta miƙa sunayen ‘yan takararta a zaɓen ƙananan hukumomin Sakkwato

PDP tana ci gaba da tattaunawa kan ko za ta shiga zaben ko a’a.

APC ta miƙa sunayen ‘yan takararta a zaɓen ƙananan hukumomin Sakkwato

APC

Jam’iyyar APC ta miƙa sunayen ’yan takararta ga Hukumar Zabe ta Jihar Sakkwato don shiga zaben kananan hukumomin jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Satumba.

Shugaban Hukumar, Alhaji Aliyu Suleiman ne ya karbi jerin sunayen, inda ya bai wa jam’iyyun siyasa tabbacin samun daidaito a lokacin gudanar da zaben.

Ya ce, “Za mu yi iyaka kokarinmu don ganin dukkan jam’iyyun siyasa sun samu gabatar da ’yan takararsu a zaben, kuma an yi musu adalci.”

Alhaji Aliyu Suleiman ya ce hukumar za ta fara tantance ’yan takarar daga jiya Alhamis 8 ga Agusta, inda ya ce tantancewar na nufin tabbatar da an gabatar da wadanda suka fi cancanta.

Ya yaba wa Jam’iyyar APC kan gabatar da jerin sunayen ’yan takararta tun kafin wa’adin da hukumar ta diba wa dukkan jam’iyyun su gabatar da ’yan takararsu.

A lokacin da yake gabatar da sunayen ’yan takarar, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Sadik Achida, ya ce sun bi duk ka’idojin da Hukumar Zaben ta shimfida wa jam’iyyun siyasa.

Alhaji Achida ya yi alkawarin bai wa hukumar goyon baya da hadin kai don ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.

Sai ya yaba wa hukumar bisa tura wakilai don ganin yadda suka gudanar da zaben fid-dagwani na jam’iyyar.

A cewar Achida, ’yan takara 23 ne suka fafata a zaben fid-da-gwani na shugabannin kananan hukumomi da kuma 244 na kansiloli.

A halin da ake ciki, babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Sakkwato tana ci gaba da tattaunawa kan ko za ta shiga zaben ko a’a.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar, Alhaji Bello Goronyo ya bayyana haka a hirar da ya yi manema labarai a Sakkwato.