APC ta musanta ficewar mambobinta masu yawa a Kano

Jam’iyyar ta ce kan ‘ya’yanta a haɗe yake kuma ta shirya wa babban zaɓen 2027.

APC ta musanta ficewar mambobinta masu yawa a Kano

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa wasu daga cikin mambobinta da dama a Ƙaramar Hukumar Kumbotso sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NDC.

Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Kano, Auwalu Soja, ya ce rahoton ba gaskiya ba ne, inda ya bayyana cewa tsarin jam’iyyar a Kumbotso yana nan daram gabanin zaɓen 2027.

Soja ya ce mutanen da ake cewa sun sauya sheƙa ba sanannun mambobin jam’iyyar ba ne, sannan ya zargi ƙungiyar Kwankwasiyya da yaɗa farfaganda domin haifar da rudani.

Ya ƙara da cewa mambobin APC a yankin suna ci gaba da goyon bayan jam’iyyar saboda ayyukan raya ƙasa da ake yi ciki har da bututun iskar gas na Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano (AKK) da layin dogo na Kaduna zuwa Kano zuwa Maradi.

Jam’iyyar ta kuma yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, kan jawo zuba jari a Kumbotso, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziƙi.

APC ta buƙaci mazauna yankin da su yi watsi da rahotannin sauya sheƙar, tana mai cewa jam’iyyar tana da haɗin kai kuma a shirye take domin zaɓen 2027.