APC ta nemi ’yan takara su yi sulhu a Kano
Gwamna Abba ya buƙaci ’yan jam’iyya su rungumi tsarin sasanci wajen fitar da ’yan takara maimakon yin zaɓen fidda gwani
Jiga-jigan Jam’iyyar APC a Jihar Kano sun yi kira da a fitar da ’yan takara ta hanyar sasanci kafin babban zaɓe mai zuwa, a matsayin mataki na ƙarfafa haɗin kan jam’iyya da kauce wa rikice-rikicen cikin gida.
An yi wannan kira ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano da yammacin Alhamis.
A jawabinsa ga ’yan jam’iyya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana taron a matsayin mai cike da tarihi, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai da sabon salo na siyasa a jihar.
“Ina amfani da wannan dama wajen gode muku bisa gudummawar da kuke bayarwa ga jam’iyya da gwamnatin jiha. Wannan taro tarihi ne domin muna da manufa iri ɗaya,” in ji shi.
- An harbe ɗan bindiga a rukunin gidajen sojoji a Abuja
- An kashe jagoran ’yan bindiga da wasu ɓarayi 4 a Zamfara
Ya ce jam’iyyar ta ƙuduri aniyar yin “siyasar mutunci, gaskiya da ci gaba,” inda tattaunawar za ta mayar da hankali kan dabarun tunkarar zaɓe mai zuwa.
Gwamna Abba ya buƙaci ’yan jam’iyya su rungumi tsarin sasanci wajen fitar da ’yan takara maimakon yin zaɓen fidda gwani.
“Muna buƙatar fahimtarku da amincewarku cewa zaɓen fidda gwani mai zuwa ya kasance cikin tsari. Ba ma son a kai ga yin ƙuri’a, sai dai sulhu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa shugabannin jam’iyya sun samu umarni da su tabbatar da an kammala sasanci a matakin jiha domin sauƙaƙa tsari, inda ya nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
“Muna son a kammala komai cikin kwana huɗu sannan a miƙa jerin sunayen ga hedikwatar jam’iyya ta kasa,” a cewarsa.
Gwamna Abba ya kuma buƙaci masu neman takara da su yi sasanci a mazaɓunsu, yana mai jaddada cewa haɗin kan cikin gida shi ne mabuɗin nasarar jam’iyya.
“Zamanin amfani da abubuwa ya wuce; muna son dukkan al’amuranmu su kasance cikin tsari,” in ji shi.
Shi ma tsohon Shugaban Jm’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga mambobin jam’iyya da su haɗa kai tare da fifita ci gaban jihar Kano.
“Dole ne mu haɗu mu amince da manufa daya. ‘Kano ce gaba da komai’ ya zama takenmu, yayin da muke kallon ci gaban jihar a hanya ɗaya,” in ji shi.
Ganduje ya amince cewa saɓani wani ɓangare ne na siyasa, amma ya buƙaci mambobin da su tafiyar da bambance-bambancen cikin hikima.
“A irin wannan lokaci, sauran jam’iyyu suna jiran su yi amfani da damar, amma hakan ba zai faru ba,” in ji shi.
Ya roƙi jiga-jigan jam’iyyar da su warware matsaloli a cikin gida tare da yin aiki tare domin ci gaba da tafiyar da jam’iyya gaba.
“Muna da fata cewa daga sama har ƙasa za mu yi nasara,” in ji Ganduje.