APC ta rasa ‘yan majalisa biyu

Jam’iyya mai mulki ta APC ta rasa ‘yan majalisar wakilan tarayya biyu saboda sanarwar da suka yi cewa, sun fita daga cikin mambobin jam’iyyar yayin da daya daga ciki ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP  a yau Laraba. ‘Yan majalisar sun sanar da fita daga cikin jam’iyyar ne bayan sun mika takardar su ga […]

APC ta rasa ‘yan majalisa biyu

APC

Jam’iyya mai mulki ta APC ta rasa ‘yan majalisar wakilan tarayya biyu saboda sanarwar da suka yi cewa, sun fita daga cikin mambobin jam’iyyar yayin da daya daga ciki ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP  a yau Laraba.

‘Yan majalisar sun sanar da fita daga cikin jam’iyyar ne bayan sun mika takardar su ga Kakakin majalisar wakilai Mista Yakubu Dogara a zauren majalisar.

‘Yan majalisar dai  sun hada da: Babatubde Kolawale, da ke wakiltar mazabar Akoko ta Arewa maso Gabas a jihar Ondo, kuma ya koma PDP. Sai kuma Dan majalisa Mukaila Kazzim, mai wakiltar mazabar Abeokuta ta Arewa/Obafemi-Owode/ da Odeda a jihar Ogun, wanda bai sanar da jam’iyyar da ya koma ba.