APC ta rusa shugabanninta a dukkan matakai

Jam’iyyar APC ta karwa wa’adin kwamitin riko na Mai Mala Buni

APC ta rusa shugabanninta a dukkan matakai

Jam’iyyar APC mai mulki ta rushe shugabanninta na dukkannin matakai kuma za ta maye gurbinsu da kwamitocin wucin gadi.

APC ta dauki matakin ne a taron gaggawan Kwamitin Zartarwarta na Kasa (NEC) ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ta kuma yi karin wata shida a kan wa’adin kwamitin rikonta kasa wanda Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ke jagoranta, daga ranar 25 ga watan Disamba da wa’adin farkon ke karewa.

Da yake jawabi bayan taron, Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce jam’iyyar ta rushe shugabanni da ba mambobin Kwamitin Gudanarawarta na Kasa (NWC) ba a matakin rumfar zabe, gunduma,  karamar hukuma, jiha da yankin siyasa.

A bayaninsa tare da Gwamnan Imo, Hope Uzodinma da Oluwarotimi Akeredolu na Jihar Ondo da kuma Sanata John James Akpanudoedehe, El-Rufai ya ce APC ta yi sassauci ga sabbin shigowa cikinta da masu shigowa a nan gaba.

Jam’iyyar ta kuma tabbatar da korar tsohon Mataimakin Shugabanta na Kasa daga Kudu-maso-Kudu, Ntufam Hilliard Eta, saboda kin janye karar da ya kai Kwamitin Rikon Kwarya na Kasa kotu.

Kwamitin Zartarwar APC ya kuma yi watsi da kiran da ake wa Shugaba Buhari ya sauka daga mukaminsa, musamman daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

A jawabinsa na bude taron, Shugaba Buhari ya ce kwamitin rikon ya dawo da kyakkyawan fata da yanayi ga jam’iyyar ta yadda wadanda suka fice suka bar ta da ma wasunsu ke ta dawowa cikinta.

Buhari ya ce abin da ya rage shi ne ci gaba da kyakkyawan aikin da kwamitin ya dauko ta hanyar tabbatar da da’a a cikin harkokin jam’iyya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos