APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa
Gabanin taron, kusoshin jam’iyyar za su gana a ranar 11 ga watan Satumba.
Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta tsayar da 12 ga watan Satumba na bana a matsayin ranar da za ta gudanar da taronta na Majalisar Zartarwa.
Mataimakin sakataren jam’iyyar, Barista Fetus Fuanter ne ya tabbatar wa manema labarai haka a yau Alhamis a Abuja.
Fuanter ya ce kusoshin jam’iyyar za su gana a ranar 11 ga watan Satumba, kafin gudanar da taron Majalisar Zartarwar a washe-gari 12 ga wata.
Taron da za a gudanar shi ne na biyu ta fuskar girma a cikin jerin tarukan da jam’iyya ke zaman yanke shawara da daukar wasu muhimman matakai bayan babban taronta na kasa.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba yada jita-jitar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sauya wa shugaban jam’iyyar na kasa muƙami.
Wasu rahotanni a bayan nan na zargin Shugaba Tinubu ya yi wa Abdullahi Umar Ganduje tayin muƙamin jakada a daya daga cikin ƙasashen nahiyar Afirka.