APC ta sake dage babban taronta zuwa shekarar 2018
Sakataren Yada Labarai na kasa na Jam’iyyar APC, Malam Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ta dage babban taronta zuwa farkon shekarar 2018. Abdullahi ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja sai dai kuma ya ce taron kwamitin shugabannin jam’iyyar da na matsu ruwa da tsaki na jam’iyyar zai gudana […]

Sakataren Yada Labarai na kasa na Jam’iyyar APC, Malam Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ta dage babban taronta zuwa farkon shekarar 2018.
Abdullahi ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja sai dai kuma ya ce taron kwamitin shugabannin jam’iyyar da na matsu ruwa da tsaki na jam’iyyar zai gudana kamar yadda aka tsara.
“Zan gaya muku cewa babban taron jam’iyyar ba zai gudana ba sai zuwa farkon shekara mai zuwa. Lokacin da babu fargabar tashin bama-bamai saboda haka ba za mu gayyaci Boko Haram zuwa taron ba”. Inji shi.