APC ta sake yin asarar Sanatoci 3
Yanzu dai adadin Sanatocin APC ya rag daga 70 zuwa 67
Sanatoci guda uku sun sake sanar da sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki.
Sanatocin sun hada da Ahmad Babba Kaita (Katsina Katsina ta Arewa) da Lawal Gumau (Bauchi ta Kudu) da kuma Francis Alimikhena (Edo ta Arewa).
Sun sanar da ficewar tasu ce a wasikun da suka aike wa Majalisar Dattawa, kuma shugabanta, Sanata Ahmed Lawan ya karanta a zauren ta ranar Talata.
Yayin da Sanata Babba Kaita da Alimikhena suka koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP, shi kuwa Sanata Gumau ya koma NNPP ne.
A wasikar Babba Kaita dai, ya ce, “A matsayina na Sanata mai wakiltar Katsina ta Arewa, na rubuto ne don sanar da sauya shekata a hukumance daga APC zuwa PDP.
“Na dauki matakin ne saboda wariyar da masu ruwa da tsakin jam’iyyar ke nuna mana a Jihar, ta yadda mutane iri na ba su isa komai ba.
“Tuni jam’iyyar PDP ta Jihar Katsina ta yi min kyakkyawar tarba,” inji wasikar.
Shi kuwa Sanata Alimikhena, ya ce ficewar tasa ta faru ne sakamakon rikicin da ya dabaibaye APC a mazabarsa tsawon lokaci, wanda ya haifar da shugabanni na tsagi daban-daban.
Da wannan sauya shekar dai, yanzu yawan Sanatocin APC ya ragu daga 70 zuwa 67. (NAN)