APC ta sanya N100m kudin sayen takardar takarar shugaban kasa

APC ta yafe wa mata da nakasassu kudin takardar neman takara

APC ta sanya N100m kudin sayen takardar takarar shugaban kasa

Sabon Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu

Jam’iyyar APC ta sanya Naira miliyan 100 a matsayin kudin takardun tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin inuwarta a zaben 2023.

Hakan na nufin an samu karin ninki biyu da kusan rabi a kan Naira miliyan 45 da aka sayar da takardun takarar a kakar zaben 2019.

Da take sanar da farashin takardun bayyana manufa da na tsayawa takarar, jam’iyyar ta ce za ta ba wa mata masu sha’awa takardar tsayawa takara kyauta, amma za su sayi fom din bayyana manufa.

Su kuma matasa masu shekara 35 zuwa kasa, ta yi musu ragin kashi 40 cikin 100 na kudin takardar tsayawa takar — Su ma za su sayi fom din bayyana manufa.

Jamiyyar ta APC ta bayyana farashin takardun bayyana aniya da kuma tsayawa takarar babban zaben 2023 a dukkanin matakai ne bayan taron majalisar gudanarwarta na farko a ranar Laraba.

Kudin takardar neman sauran kujerun su ne:

  • Gwamna – Naira miliyan 50
  • Majalisar Dattawa – Naira miliyan 20
  • Majalisar Wakilai – Naira miliyan 10
  • Majalisar Jiha – Naira miliyan biyu.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna