APC ta shiga Jihar Kebbi da kafar dama – danmalikin Kabi

Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi Alhaji Musa Abubakar ya ce jam’iyyar ta shiga jihar da kafar dama idan aka yi la akari da yadda ta samu karbuwa a wurin talakawa lungu da sakon kananan hukumomi 21 dake jihar.Alhaji Musa Abubakar wanda har wa yau shi ne danmalikin Kabi yya bayyana haka ne […]

APC ta shiga Jihar Kebbi da kafar dama – danmalikin Kabi
APC ta shiga Jihar Kebbi da kafar dama – danmalikin Kabi

Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi Alhaji Musa Abubakar ya ce jam’iyyar ta shiga jihar da kafar dama idan aka yi la akari da yadda ta samu karbuwa a wurin talakawa lungu da sakon kananan hukumomi 21 dake jihar.
Alhaji Musa Abubakar wanda har wa yau shi ne danmalikin Kabi yya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishin jam’iyyar da ke hanyar Go Slow a cikin Birnin Kebbi.
Ya ce, jam’iyyar ta samu karbuwa ne sakamakon yadda jama’a suka yarda da jagororin jam’iyyar daga sama na kasancewa masu gaskiya da akidar tausaya wa al’umma da kawo zaman lafiya da rashin nuna bambancin kabila ko addini ko bangare.
danmalikin Kabin ya ce al’ummar Jihar Kebbi sai hamdala saboda sun samu shugabannin da za su ceto su daga halin kaka-ni-ka yi da suka shiga na rashin kyakkyawan shugabanci da talaucin da suke ciki, “kuma canji na alheri na daf da samuwa,” inji shi.
Ya ce jama’a na ta tururuwar shiga Jami’yyar APC a jihar ciki har da wasu shugabannin PDP amma ba za su bayyanansu ba sai nan gaba.
 Alhaji Abubakar ya ce da yardar Allah 2015 gwamnatin APC ne za a rantsar a Jihar Kebbi, “Rashin adalcin Jam’iyyar PDP tun daga shugabanninta na kasa zuwa jihohi da kananan hukumomi ne ya sa jama’a ke fita daga cikinta suna komawa APC, a yanzu PDP ta zama fanko ba nauyi,” inji shi.