APC ta tantance ‘yan takarar Gwamnan jihar Kogi 12

Kwamitin mutum shida na jam’iyyar APC wanda Sanata Hope Uzodimma ke jagoranta sun tantance ‘yan takarar neman Gwamnan jihar Kogi 12 cikin 16 da suke neman zama wanda zai tsaya a matsayin dan takarar Gwamnan jihar daga APC. An dai fara tantance Gwamna mai ci Yahaya Bello da Misis Ekele Blessing da Injiniya Abubakar Bashir […]

APC ta tantance ‘yan takarar Gwamnan jihar Kogi 12

Kwamitin mutum shida na jam’iyyar APC wanda Sanata Hope Uzodimma ke jagoranta sun tantance ‘yan takarar neman Gwamnan jihar Kogi 12 cikin 16 da suke neman zama wanda zai tsaya a matsayin dan takarar Gwamnan jihar daga APC.

An dai fara tantance Gwamna mai ci Yahaya Bello da Misis Ekele Blessing da Injiniya Abubakar Bashir da dan majalisar wakilan tarayya Hassan Abdullahi.

Akwai rahoton da ke bayyana cewa, ba a kammala bincike game da sunayen wasu masu neman takarar Gwamna a APC da aka mikawa shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ba, wadanda suka hada da: Usman Oyibe Jibrin, Farfesa Mohammed Seidu Onailu, Mustapha Mona Audu, Hadiza Iyoma Ibrahim, Yahaya Odidi Audu, Sani Lulu Abdullahi, Janar Patrick Adenu Akpa, Injiniya Danlami Umar Mohammed, Yakubu Mohammed, Babatunde Ayo Kunle Irukera, Rukkaya Ibrahim da Mohammed Abubakar Audu.