APC ta yi barazanar dakatar da Danjuma Goje a Gombe
APC na zarginsa da ba da umarnin a zabi wasu ba mambobinta ba
Jam’iyyar APC ta yi barazanar dakatar da Sanatan Gombe ta Tsakiya, Mohammed Danjuma Goje saboda yi mata angulu da kan zabo a zabukan da suka gabata.
Shugaban jam’iyyar na gundumar Kashere, inda nan ne mazabar Sanatan, Tanimu Abdullahi Kashere, ya ce sun kafa kwamiti dan tuhumar shi kan zarge-zarge.
- APC a Jihar Adamawa ta dakatar da Boss Mustapha daga cikinta
- An ga watan Ramadan a Najeriya – Sarkin Musulmi
Tanimu Kashere, ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Laraba, inda ya ce a matakin gunduma suka kafa kwamitin na mutum biyar dan gurfanar da Sanatan.
Ya ce suna zarginsa da cewa a lokacin zaben Shugaban Kasa da na Gwamnoni, ya ba da umurni a yi wata jam’iyyar ba jam’iyyarsa ta APC ba.
Tanimu ya kuma ce Sanatan ya bai wa magoya bayansa umurni a lokacin zaben shugaban kasa kan su zabi jam’iyyar PDP ba APC ba, haka a zaben Gwamna ma ya ce a yi PDP, sannan a dan Majalisar Jihar ya ce a zabi jam’iyyar PRP.
A cewarsa, “Kana wata jam’iyya ka ce a zabi dan takarar da ba na jam’iyyarka ba, hakan ba dai dai ba ne. Mun ba ’yan kwamitin mako biyu su gurfanar da shi ya yi musu bayani.
“Idan kuma aka samu akasin haka, jam’iyya za ta dauki matakin dakatar da shi,” in ji Shugaban na APC.
Ya kuma ce ba Goje ne kadai suke zargi da yin angulu da kan zabon ba, akwai wasu ’ya’yan jam’iyyar ma wadanda idan zargin da ake musu ya tabbata za su fuskanci fushinta.
Daga nan sai yace yanzu dai sun bar ’yan kwamiti suyi aikinsu, su binciko gaskiyar lamarin kafin su kuma su yanke hukunci.