APC ta yi mulkin kama-karya na shekara 8 a Kaduna — Shehu Sani

Kar Tinubu ya saki jiki da El-Rufai domin ba shi da maraba da dan maciji.

APC ta yi mulkin kama-karya na shekara 8 a Kaduna — Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya koka kan abin da ya bayyana a matsayin mulkin kama-karya na tsawon shekara takwas da jam’iyyar APC ta yi a Jihar Kaduna.

Sani wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a Kaduna, ya kuma nuna damuwarsa kan bita-da-kulli da ‘yan adawar siyasar jihar ke yi masa.

Da yake kokawa kan harin da aka kai ofishin yakin neman zabensa, ya ce: “’Yan bindiga sun kai hari ofishina, an kuma yi amfani da ‘yan barandan APC suka rinka bi na duk inda na je. Sun kuma umarci sojoji da su kama daya daga cikin mataimakana, Bashir Ahmad, a 2017.

“Sojoji sun azabtar da Bashir don tilasta masa ya min sharrin kisan kai da ba ni da masaniya a kai. ‘Yan sanda sun yi watsi da karar bayan da suka gano siyasa ce kawai.”

Ya bayyana cewa a shekara takwas da Gwamna Nasir El-Rufai ya shafe yana jagorantar Jihar Kaduna, babu abin da ya yi face almubazzaranci da baitul mali wanda ke tattare da kunci, tsantsar mugunta da zalunci.

Sani ya gargadi Shugaban Kasa Bola Tinubu a kan abin da ya kira irin “soyayya” da mu’amalar da tsohon gwamnan na Kaduna ke nuna masa.

“Tafiyar El-Rufai samun sauki ne. Ya kamata Tinubu ya yi taka-tsan-tsan ka da ya jawo shi jikinsa, saboda dan maciji ne,” in ji shi.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro