APC ta yi nasarar kawo canji a Najeriya – Hajiya dambatta

Wata jigo a Jam’iyyar APC daga karamar Hukumar dambatta, Hajiya Alpha Abdu Usman dambatta ta ce gwamnatin jam’iyyar APC tana samun kyawawan nasarori wajen kawo managarcin canji a wannan kasa tun bayan zaben 2015. Ta yi wannan bayani ne a zantawarta da Amniya, inda ta nunar da cewa daga wancan lokaci zuwa yau an sami […]

APC ta yi nasarar kawo canji a Najeriya – Hajiya dambatta

Wata jigo a Jam’iyyar APC daga karamar Hukumar dambatta, Hajiya Alpha Abdu Usman dambatta ta ce gwamnatin jam’iyyar APC tana samun kyawawan nasarori wajen kawo managarcin canji a wannan kasa tun bayan zaben 2015.

Ta yi wannan bayani ne a zantawarta da Amniya, inda ta nunar da cewa daga wancan lokaci zuwa yau an sami nasarori wajen canza wasu al’amura a kasa baki daya, wanda hakan ya nuna cewa APC ta na da manufofi kyawawa, sannan za ta yi nasarar bunkasa tattalin arzikin kasa da inganta rayuwar al’umar kasa.

Ta ce masu ganin gazawar wannan gwamnati ba su fahimci yadda al’amura suke tafiya ba ne, amma nan gaba kadan kowa zai fahimci cewa APC ce ta ke da tsari da kuma manufofi masu nagarta wajen farfado da darajar Najeriya bisa la’akari da irin salon shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Haka kuma ta yi nuni da cewa a cikin shekaru biyu na gwamnatin Buhari, kowa ya ga yadda kasar nan ta ke kara samun daraja da martaba a idon duniya musamman ganin yadda ake tafiyar da al’amuran kasa cikin tsari da dora kasar nan bisa ginshiki mai inganci domin kyautata zamantakewar al’uma ta kowane fanni.

A matakin Jihar Kano kuwa, Hajiya Alpha Abdu Usman dambatta ta nuna gamsuwar ta dangane da yadda gwamnatin jihar bisa jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje take aiwatar da shugabanci na adalci da gudanar da aikace-aikace masu matukar amfani ga al’umar jihar bisa yin la’akari da bukatun kowane bangare dake fadin jihar.

Dangane da maganar janye sunanta da aka yi a mukamin kansila, dambatta ta ce wannan abu sam bai karya mata gwuiwar zama a cikin jam’iyyar APC ba, sannan ta san cewa komai a hannun Allah yake, don haka babu wani abu da zai hana ta tafiya da kowa a siyasance.